El Rufai Ya Saurari Wayar Nuhu Ribadu, Ya Gano Wanda Ya bada Umarnin a Kama Shi
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi ikirarin cewa sun saurari wayar mai ba shugaban kasa shawara kan taaro, Nuhu Ribadu
- El-Rufai ya yi zargin cewa Nuhu Ribadu da kansa ya ba da umarnin a kama shi a tsare shi idan ya dawo Najeriya daga kasar waje
- Hadimin shugaban kasa ya nuna damuwa kan kalaman Malam El-Rufai, yana mai cewa ya san abin da suka yi ya sabawa dokar kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya zargi Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, da bayar da umarnin kama shi.
El-Rufai ya kuma zargi Nuhu Ribadu da hannu a yunƙurin kama shi a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Alhamis lokacin da ya dawo daga kasar Masar.

Source: Facebook
El-Rufai ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise TV a ranar Juma’a, inda ya yi zargin cewa Ribadu ne da kansa ya bayar da umarnin a kama shi.
Tun da farko, jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an yi cacar baki tsakanin El-Rufai da jami’an tsaro a filin jirgin saman Abuja jim kaɗan bayan isowarsa ƙasar.
Rahotanni daga shaidu sun ce jami’an tsaro sun riƙe shi na ɗan lokaci tare da ƙwace fasfonsa, kafin daga bisani a bar shi ya fita daga filin jirgin saman, a yayin da magoya bayansa ke yi masa sannu da zuwa.
Zargin sauraron wayar Nuhu Ribadu
El-Rufai ya kuma yi zargin cewa an saurari kiran wayar NSA Nuhu Ribadu, inda ya ce sun ji shi yana umartar jami’an tsaro da su tsare shi.
“An saurari kiran wayar NSA, su ma suna bibiyar kiraye kirayen da muke yi, kuma mun ji shi yana cewa su kama ni,” in ji El-Rufai.
Sai dai bai gabatar da wata hujja da ke tabbatar da zargin ba, kuma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga Nuhu Ribadu kan zargin.

Source: Twitter
Fadar shugaban kasa ta yi magana
A nata ɓangaren, fadar shugaban ƙasa ta nuna damuwa kan kalaman El-Rufai game da sauraron wayar Nuhu Ribadu.
Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Midiya, Temitope Ajayi, ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa:
“El-Rufai ya yi furuci a talabijin cewa wani ya saurari wayar NSA domin shi ya ji hirar. Lokacin da mai gabatar da shirin, Charles Aniagolu, ya fada masa hakan haramun ne a doka, El-Rufai ya amince haram ne.
"Yanzu idan aka kama shi aka nemi ya fito da wanda ya aikata wannan laifi, zai ce Shugaba Tinubu azzalumi ne kuma ana tsananta masa.”
El-Rufai zai fito takara a zaben 2027?
A wani labarin, kun ji cewa Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ba shi da wani shiri na yin takarar shugaban kasa a 2027, amma bai kore yiwuwar takarar ba.
Tsohon gwamnan ya ce akwai wadanda suka cancanci yin takara fiye da shi, amma kuma zai iya neman kujerar shugaban kasar bisa wasu dalilai.
El-Rufai mai shekara 65 ya bayyana cewa duk da matsalolin da ƙasar nan ke fuskanta, har yanzu bai yanke shawarar tsayawa takara a hukumance ba.
Asali: Legit.ng

