Zargin Amurka: NNPP Ta Jingine Siyasa, Ta Tura Bukata ga Shugaba Tinubu kan Kwankwaso

Zargin Amurka: NNPP Ta Jingine Siyasa, Ta Tura Bukata ga Shugaba Tinubu kan Kwankwaso

  • NNPP ta roki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mai bada shawara kan tsaron kasa (NSA) su wanke Sanata Rabiu Kwankwaso daga zargin Amurka
  • Mai magana da yawun NNPP na Kano, Ibrahim Karaye ya ce Kwankwaso mutum ne mai kishin kasa kuma hudimar da ya yi wa jama'a ta nuna haka
  • NNPP ta roƙi Shugaban Ƙasa da NSA su gaggauta fitar da sanarwa a hukumance domin wanke Kwankwaso daga zargi mara tushe da ake yi masa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano ta jingine duk wani sabanin siyasa, ta roki fadar shugaban kasa ta fito ta wanke jagora Dr. Rabiu Musa Kwankwaso daga zargin Amurka.

NNPP ta kuma roki ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) ya sa baki wajen wanke Kwankwaso daga zargin da 'yan Majalisar Amurka suka masa na tauye hakkin addini.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP ta kunnowa Kwankwaso wata wuta kan zargin da Amurka ke yi masa

Kwankwaso.
Jagoran NNPP kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na NNPP a jihar Kano, Injiniya Ibrahim Karaye, ya sanya wa hannu ranar Juma'a, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Idan baku manta ba yan Majalisar Amurka hudu sun gabatar da wani kudiri, wanda a cikinsa aka ga sunan Kwankwaso cikin wadanda ake zargi da take hakkin addini.

Jam'iyyar NNPP ta roki Tinubu da NSA

NNPP ta roƙi shugaban kasa da NSA su gaggauta fitar da sanarwa a hukumance domin wanke Kwankwaso daga abin da ta kira zarge-zarge marasa tushe.

Jam’iyyar ta bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan Najeriya mai kishin ƙasa, tana mai cewa tarihin aikinsa a fannin ilimi da yiwa talakawa hidimi ya isa shaida a kansa

“NNPP na sake jaddada cewa jagoranmu na kasa mutum ne mai kishin ƙasa, wanda hakan ya fito fili a yadda ya ba da gudummuwa a fannin ilimi da haɓaka ɗan Adam,” in ji sanarwar.

Kara karanta wannan

An 'gano' dalilin zargin Amurka kan Kwankwaso bayan martani ga matakin Trump

NNPP ta yi gargaɗi kan siyasantar da batutuwan da suka shafi tsaro, tana mai cewa bai kamata a yi amfani da irin wannan zarge-zarge a matsayin makamin yaki a fagen siyasa ba.

Sakon jam'iyyar NNPP ga 'yan Najeriya

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya su yi Allah-wadai da abin da ta kira ƙoƙarin ɓata sunan jagoranta ta hanyar zarge-zarge marasa tabbas, cewar rahoton This Day.

Ta kuma yi nuni da yunkurin ƙasashen waje, ciki har da Amurka, na ɗaukar matakai bisa zarge-zargen kage, tare da kira da a yi taka-tsantsan da cikakken bincike kan irin waɗannan batutuwa masu muhimmanci.

Kwankwaso da Shugaba Tinubu.
Jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso tare da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

NNPP ta ce matakan da Kwankwaso ya dauka a aiyasa, ciki har da ƙin komawa jam’iyyar APC saboda bambancin manufofi, bai kamata a juya su zuwa zarge-zargen da suka shafi tsaro ba.

A ƙarshe, jam’iyyar NNPP ta buƙaci Fadar shugaban Ƙasa da Ofishin NSA su gaggauta fayyace matsayar gwamnati domin kauce wa abin da ta kira kunyatar da ƙasa da kuma bata suna a idon duniya.

Kwankwasiyya ta aika sako Amurka

A wani labarin, kun ji cewa Kwankwasiyya ta aika sako Amurka bayan sanya sunan Kwankwaso a jerin wadanda kasar ke zargi da hannu a tauye hakkin addini a Najeriya.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Gwamnatin Abba ta yi magana kan batun hana Kwankwaso zuwa Kano

Kwankwasiyya ta bayyana saka sunan tsohon gwamnan Kano a cikin kudirin yan Majalisar Amurka a matsayin kage marar tushe.

Ta buƙaci Majalisar Dokokin Amurka ta cire sunan Kwankwaso cikin kudirin, tana mai zargin cewa wasu na iya amfani da lamarin wajen biyan buƙatun siyasa ko ramuwar gayya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262