An ‘Gano’ Dalilin Zargin Amurka kan Kwankwaso bayan Cacar Baki da Dan Majalisa

An ‘Gano’ Dalilin Zargin Amurka kan Kwankwaso bayan Cacar Baki da Dan Majalisa

  • Wasu majiyoyi sun ce saka sunan Rabiu Musa Kwankwaso a kudirin dokar Amurka kan ‘yancin addini zalunci ne ba tare da hujja ba
  • An ce rikicin ya samo asali ne daga muhawarar Kwankwaso da dan majalisar Amurka Riley Moore a dandalin X
  • Ana fargabar cewa amfani da dokar kasashen waje don muzgunawa ‘yan adawa barazana ce ga ikon Najeriya da zaman lafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ana ci gaba da korafi kan saka sunan Rabiu Kwankwaso cikin jerin masu tsattsauran ra'ayin addini a Najeriya.

Wasu majiyoyi suka ce saka sunan tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, a cikin kudirin dokar Amurka kan ‘yancin addini ba komai ba ne illa zalunci da farautar siyasa.

An zargin dalilin zargin Kwankwaso da Amurka ke yi
Dan majalisar Amurka da Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Hoto: RMKwankwaso/RepRileyMoore.
Source: Twitter

Rahoton Zagazola Makama ya ce hakan na cikin kudirin mai taken 'Nigeria Religious Freedom and Accountability Act of 2026'.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan Kano ya aika sako ga majalisar Amurka kan zargin da ake yi wa Kwankwaso

Kudirin da aka kira sunan Kwankwaso a ciki

Kudirin wanda dan majalisar Amurka Riley Moore da Chris Smith suka dauki nauyi, ya nemi kakaba takunkumi kan Fulani da kuma Kwankwaso bisa zargin tsananta wa Kiristoci.

Sai dai masu sukar matakin sun ce an janyo sunan Kwankwaso ne bayan musayar kalamai da Moore a shafin X, ba tare da wata kwakkwarar hujja da ke nuna hannunsa a take hakkin addini ba.

Rahoton ya ce rikicin ya biyo bayan matakin Shugaban Amurka Donald Trump na ayyana Najeriya a cikin jerin kasashe karkashin CPC kan batun ‘yancin addini.

Kwankwaso ya mayar da martani a X inda ya nuna damuwa kan kalaman Trump, yana mai cewa irin wadannan furuci na iya kara rarrabuwar kawuna maimakon magance matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta.

Ya ce Najeriya kasa ce mai cikakken iko, kuma barazanar da ake fuskanta daga kungiyoyin ta’addanci ba ta ware addini, kabila ko siyasa ba.

Kara karanta wannan

Amurka: 'Dan majalisar Kano ya faɗi mataki na gaba a kan yi wa Kwankwaso 'kazafi'

“Abin da Najeriya ke bukata shi ne tallafi ta fuskar fasaha, bayanan sirri da karfafa aiki, ba kalaman da za su kara rarrabuwa ba,”

- In ji Kwankwaso

Zargin Amurka kan Kwankwaso ya jawo maganganu a Najeriya
Jagoran siyasar Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Zargin da Riley Moore ya yi ga Kwankwaso

A martaninsa, Moore ya zargi Kwankwaso da hannu a mutuwar Kiristoci, yana mai alakanta rattaba hannunsa kan dokar Shari’a a Kano da batun take hakkin addini.

Sai dai an ce alakanta dokar Shari’a da ayyukan Boko Haram da ‘yan bindiga kuskure ne, domin Shari’a wani bangare ne na tsarin tarayyar Najeriya, ba ta’addanci ba ne, cewar TheCable.

Ya kuma jaddada cewa a zamanin mulkin Kwankwaso, jihar Kano ta dakile shigowar kungiyar Boko Haram tare da rusa hanyoyin daukar ma’aikata da kayayyaki, lamarin da ya hana kungiyar kafa gindin zama a jihar.

Kwankwaso: Mataimakin gwamna ya tura sako ga Amurka

An ji cewa har yanzu ana ci gaba da magana kan yunkurin wasu 'yan majalisar dokokin Amurka na ganin an kakabawa Rabiu Musa Kwankwaso takunkumi.

Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya bayyana cewa Kwankwaso bai da tarihin muzgunawa mutanen da ba addininsu daya ba.

Gwarzo ya bukaci majalisar dokokin Amurka da ta cire sunan Kwankwaso daga cikin kudirin dokar da aka gabatar a gabanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.