‘Ba Shi Kadai Ya Kafa Shari’a ba’: An ‘Gano’ Shirin Amurka kan Siyasar Kwankwaso

‘Ba Shi Kadai Ya Kafa Shari’a ba’: An ‘Gano’ Shirin Amurka kan Siyasar Kwankwaso

  • Mai fashin baki a siyasa, Mahdi Shehu ya yi magana kan ayyana Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin mai tsattsauran ra’ayi
  • Ya danganta ayyana Kwankwaso da wasu sauye-sauyen siyasa da suka faru, ciki har da sauya sheƙar gwamnan Kano da tattaunawar takarar mataimaki
  • Mahdi Shehu ya yi zargin cewa ana iya yin irin wannan sharri ga Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai da sauran jagororin adawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wani mai fashin baki kan harkokin siyasa, Mahdi Shehu, ya yi magana game da korafin da Amurka ta yi kan Rabiu Kwankwaso.

Mahdi ya bayyana cewa ayyana Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin mai tsattsauran ra’ayin addini wani shiri ne da aka tsara domin rage masa karfi a siyasa da kuma raunana adawa.

An kare Kwankwaso kan zargin da Amurka ta yi masa
Sanata Rabiu Kwankaso da Shugaba Donald Trump. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Donald J Trump.
Source: Facebook

'Shirin da Amurka ta yi kan Kwankwaso'

Kara karanta wannan

Yadda alakar El-Rufai da Ribadu ta lalace shekaru bayan yi masa takwara

Mahdi Shehu ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce ana yi wa jagororin adawa lakabi da nufin bata musu suna a idon duniya.

Mahdi ya bayyana cewa ba kuskure ba ne ayyana Kwankwaso a matsayin mai tsauttsauran ra'ayin addini inda ya ce bai da tarihin haka.

Ya ce:

“Gaskiyar magana, ana ayyana Kwankwaso a matsayin mai tsattsauran ra’ayi alhali an san ba shi da wannan tarihin, ba kuskure ba ne, wani tsari ne na rage masa tasiri a siyasa.”

Sannan ya ce akwai wata alaka ta tsakanin wasu muhimman abubuwan siyasa da kuma ayyana Kwankwaso da aka yi.

Mahdi Shehu ya kare Kwanwaso game da zargin Amurka
Rabiu Kwankwaso, Mahdi Shehu da Donald Trump. Hoto: @KwakwasoRM, @shehu_mahdi, @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Zargin dalilin kakaba wa Kwankwaso 'sharri'

Ya misalta cewa makonni biyu bayan wasu tattaunawa na kasa da kasa da sauyin sheƙar gwamnan Kano, an bayyana Rabiu Kwankwaso a matsayin mai tsattsauran ra’ayi.

Ya kara da cewa idan sanya hannu kan dokar Shari’ar laifuffuka a Kano ne dalili, to ya kamata a kira duk gwamnonin Arewa da suka rattaba hannu kan dokokin Shari’a a lokacin Olusegun Obasanjo da sunan masu tsattsauran ra’ayi.

Kara karanta wannan

Karamar magana ta zama babba, Kwankwasiyya ta aika sako ga majalisar Amurka

“Idan ayyana Kwankwaso a matsayin ‘mai tsattsauran ra’ayin Musulunci’ ya samo asali ne daga rattaba hannunsa kan Dokar Hukunta Laifuka ta Shari’a a Kano lokacin yana gwamna, to hakan na nufin dukkan gwamnonin jihohin Arewa da suka sanya hannu kan dokokin Shari’a a lokacin da kuma bayan mulkin Obasanjo su ma za a kira su masu tsattsauran ra’ayi. Wannan ya hada da gwamnonin Zamfara, Katsina, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Bauchi, Jigawa, Gombe, Borno da Yobe."

- Cewar Mahdi

Mahdi Shehu ya kuma ambaci cewa makonni biyu bayan wasu manyan ‘yan siyasa sun gana da Kwankwaso, sai aka sake jaddada wannan sharri a kansa, abin da ya ce ba daidaito ba ne illa wata dabara ta siyasa kafin zaben 2027.

Ya yi gargadin cewa ana iya yin irin wannan sharri kan wasu jagororin adawa kamar Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai, ta hanyar jingina musu daukar nauyin ta’addanci.

A cewarsa, duk wadannan zarge-zarge da ake jingina wa jagororin adawa, na cikin abin da ya kira yaki da adawa wanda daga karshe gaskiya za ta bayyana.

Kwankwaso: Kwankwasiyya ta tura sako ga Amurka

Mun ba ku labarin cewa Kwankwasiyya ta aika sako Amurka bayan sanya sunan Kwankwaso a jerin wadanda kasar ke zargi da hannu a tauye hakkin addini a Najeriya.

Tafiyar Kwankwasiyya ta bayyana cewa ba a jihar Kano kadai aka kaddamar da shari'a ba, don haka ware mutum daya ba adalci ba ne.

Ta bukaci majalisar dokokin Amurka ta gaggauta cire sunan Kwankwaso daga cikin kudirinta domin hakan na iya yi masa illa a siyasance.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.