Sanata Ahmad Babba Kaita: Yadda Masoya Suka Hana Jami'ai Tafiya da El Rufa'i

Sanata Ahmad Babba Kaita: Yadda Masoya Suka Hana Jami'ai Tafiya da El Rufa'i

  • Tsohon Sanata, Ahmad Babba Kaita ya ce jama’a ne suka hana kama tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i a Abuja
  • A ranar Alhamis 13 ga watan Fabrairu na shekarar 2026 ne wasu jami'ai suka dura a filin jirgin Abuja bayan El-Rufa'i ya shigo kasar
  • Jama'a sun yi cincirindo, suka ce uban kuturu ya yi kadan, babu mai tafiya da tsohon gwamnan sai ya isa gidansa laifya kalau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna –Tsohon Sanata mai wakiltar Katsina ta Arewa, Ahmad Babba Kaita, ya bayyana cewa jama’a da magoya baya sun dakile yunkurin wasu jami’an tsaro a kan Nasir El-Rufa'i.

Ya bayyana cewa masoya da magoya baya ne suka yi tsayin daka a lokacin da wasu jami'ai suka yi niyyar cafke tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a filin jirgin sama na Abuja.

Kara karanta wannan

Atiku ya ki shiru, ya dura kan Tinubu da EFCC a kan kama El Rufa'i da 'yan ADC

Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya tsira daga kamun jami'an gwamnati
Nasir El-Rufa'i a lokacin da ya ke gwamnan Kaduna Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Sanatan ya bayyana haka ne a hira da ya yi da DCL Hausa jim kadan bayan an raka Naiar El-Rufa'i gidansa a cikin koshin lafiya.

Jami’ai sun yi niyyar kama El-Rufa’i a filin jirgi

Ahmad Babba Kaita ya ce su ne suka fara zuwa domin tarbar Nasir El-Rufa’i bayan dawowarsa daga ƙasar waje.

A cewar tsohon Sanatan na Arewacin Katsina, a daidai lokacin da tsohon gwamnan ya sauka ne jami’an suka tare su tare da nuna aniyar kama shi.

El-Rufa'i ya zargi gwamnati da kama yan adawa
Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i a wani taron ADC Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Twitter

A kalamansa, Sanatan ya ce:

“Yana sauka sai aka samu wadansu wanda aka ce an turo daga wuraren daban-daban. Wasu sun ce daga NSA wasu daga Fadar Shugaban kasa.”
“Suka ce Malam Nasir El-Rufa’i ba zai fito ba, muka wannan kuma uban kuturu ya yi kaɗan.”
“Malam Nasiru dan Najeriya ne, kuma yana da yanci. Kuma ba a gayyace shi ba, ba a rubuto masa takarda ba.”

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya ce rikicin duniya da mai rai ake yi , zai buga da Tinubu da APC

Sanatan ya jaddada cewa babu wata takarda ta gayyata ko sammaci da aka nuna musu, lamarin da ya sa suka ga yunkurin a matsayin take hakkin dan kasa.

Jama’a sun tsaya wa Malam El-Rufa'i

Babba Kaita ya kara da cewa jama’a da magoya bayan El-Rufa’i ne suka shiga tsakani, lamarin da ya hana jami’an tsaron cimma manufarsu.

Ya zargi jami’an da kokarin tozarta El-Rufa’i a bainar jama’a, yana mai cewa ana amfani da irin wannan dabara wajen wulakanta wasu ‘yan adawa a Najeriya.

A cewarsa, kamata ya yi hukumomi su bi doka da oda idan har suna da wata magana ko zargi a kan duk wani dan kasa, maimakon amfani da salon da zai janyo cece-kuce a idon jama’a.

Kaita ya bayyana cewa jami’an da suka iso wurin sun shaida masu cewa an turo su ne daga ofishin Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), yayin da wasu kuma suka ce daga Fadar Shugaban ƙasa suka fito.

Ana kokarin cafke ni - El-Rufa'i

A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi maganar da ke nuna cewa zai iya shiga hannun hukumomin Najeriya a nan gaba.

Kara karanta wannan

Bayan abin da ya faru a filin jirgi, El Rufai zai gurfana a gaban hukumar EFCC

El-Rufa’i, da ya yi magana daga Cairo, ya bayyana hakan ne bayan ya lura da yadda aka kama wasu daga cikin wadanda suka yi aiki tare da shi a lokacin da yake gwamna a jihar Kaduna.

Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa wannan ba zai zama sabon abu ba, inda ya yi zargin gwamnati tana amfani da kama wadanda ba sa goyon bayanta wajen murkushe yan adawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng