Yadda Alakar El Rufai da Ribadu Ta Lalace Shekaru bayan Yi Masa Takwara

Yadda Alakar El Rufai da Ribadu Ta Lalace Shekaru bayan Yi Masa Takwara

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya zargi APC da zalunci bayan ficewarsa zuwa ADC, yana mai cewa ana yi masa bita da kulli a siyasa
  • El-Rufai ya nuna mamaki kan sauyin halayen Malam Nuhu Ribadu duk da kyakkyawar alakar da suka taba yi a baya wanda ya sauya a yanzu
  • Ya ce “ruwa ba zai ci El-Rufai ba,” yana mai jaddada cewa Allah na tare da shi, tare da kalubalantar Ribadu ya bayyana dalilin da ake zarginsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna ya magantu kan yadda siyasar Najeriya ke tafiya a halin yanzu karkashin jagorancin APC.

El-Rufai ya nuna damuwa ka bita da kulli da ake yi masa tun bayan ficewa daga jamiyya mai mulki zuwa ADC saboda zaluncinsu.

El-Rufai ya caccaki Nuhu Ribadu alakarsu a baya
Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai. Hoto: Nasir El-Rufai.
Source: Twitter

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a bidiyo yayin hira da BBC Hausa wanda aka wallafa a Facebook a yau Juma'a 13 ga watan Faburairun 2026.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya ce rikicin duniya da mai rai ake yi , zai buga da Tinubu da APC

El-Rufai ya kadu kan yadda Ribadu ya sauya hali

A cikin bidiyon, El-Rufai ya bayyana mamakinsa kan halayen Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu duk da alaka mai kyau da suke da shi a baya.

Ya ce a yadda ya san Ribadu a baya, kwata-kwata a yanzu kamar ba shi ba saboda yadda suka yi alaka mai kyau da shi a baya.

Ya ce:

"Kwarai ina da alaka mai kyau da Ribadu a baya, dan autan shi ma sunansa Nasiru kuma don ni ya sa."
Alakar Ribadu da El-Rufai ta sake wargajewa
Malam Nuhu Ribadu da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai. Hoto: Nuhu Ribadu, Nasir El-Rufai.
Source: Twitter

El-Rufai ya yi alfahari da siyasarsa

An tambayi El-Rufai duba da yawan zargin Ribadu da bita da kullin siyasa ga yan adawa, anya ba ruwa ne zai ci El-Rufai ba kuwa?

Sai El-Rufai ya kada baki ya ce:

"Ruwa ba zai ci El-Rufai ba domin Allah yana tare da ni, abin yana kona min rai idan na yi tunanin mutumin da na dauka mutumin kirki ne amma yanzu ya zama wani abu ban ma iya fahimtar shi.

Kara karanta wannan

Gwamna na tsaka mai wuya game da maye gurbin mataimakinsa da ya mutu

"Duk wadannan abubuwan idan Allah ya yarda za su koma kan shi."
"Nuhu Ribadu aikin gwamnati ne ya hada mu, idan kin same shi ki tambaye shi me yasa ya saka wa dan autan shi Nasiru."

Wannan ya biyo bayan yawan korafi da El-Rufai ke yi kan Nuhu Ribadu wanda ake zargin ko akwai takun-saka a tsakaninsu wanda ya tabbatar a wannan hira da aka yi da shi.

Atiku ya ziyarci El-Rufai bayan yunkurin kama shi

Mun ba ku labarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kai ziyarar goyon baya ga tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Atiku ya nuna masa cikakken goyon baya, yana zargin gwamnatin Bola Tinubu da kokarin kawo mulkin kama-karya da neman daile yancin dimukradiyya.

Ziyarar na zuwa ne bayan kokarin jami’an tsaro na cafke El-Rufai, lamarin da ya haddasa ce-ce-ku-ce da rikici wanda ake ganin bita da kullin siyasa ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.