El Rufa'i Ya Ce Rikicin Duniya da Mai Rai ake, zai Buga da Tinubu da APC
- Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce jami’an tsaro sun yi yunƙurin kama shi a filin jirgin sama na Abuja bayan dawowarsa daga Masar
- A hirar da aka yi da shi, El-Rufa'i ya bayyana cewa ya nemi jami'an DSS su nuna masa takardar gayyata amma ba a gabatar masa da ita ba a lokacin
- Tsohon gwamnan ya ce ba zai daina adawa da gwamnati ba duk da bita da kulli da ake masa, ya ce rikicin duniya da mai rai ake, kuma zai cigaba da fafatawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce bita da ƙulli da zai hana shi ci gaba da adawa da gwamnatin Bola Tinubu ba.
El-Rufai ya bayyana haka ne bayan wani lamari da ya faru a ranar Alhamis, 12 ga Faburairu, 2026, lokacin da jami’an tsaro suka yi yunƙurin kama shi a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja bayan dawowa daga Masar.

Source: Facebook
A hirar da ya yi da BBC Hausa, El-Rufa'i ya ce gwamnatin Bola Tinubu bata kauransa kuma da tana da wani dalili na kama shi da tuntuni ta cafke shi.
Maganar cafke El-Rufa'i a Abuja
El-Rufai ya bayyana cewa kokarin kama shi ya samo asali ne lokacin da wani jami’i ya tunkare shi yana mai cewa sun fito ne daga hukumar DSS kuma suna son ya je ofishinsu.
A cewarsa:
“Ina sauka daga jirgi wani ɗan matashi ya zo da wata ƙaramar jaka ya ce su sun zo daga DSS kuma suna son su ganni a ofishinsu. Sai na ce ina takarda? Sai ya ce za a ba da takarda.
“Da muka fito sai shugabanninsa suka zo suka maimaita maganar. Na ce takarda za ku ba ni.
'Ruwa ba zai karewa El-Rufa'i ba'
El-Rufai ya bayyana abin da ya faru a matsayin yunƙurin tauye masa haƙƙinsa na ɗan Adam, yana mai cewa kundin tsarin mulkin Najeriya bai yarda da kama ko gayyatar mutum ba tare da bin ƙa’ida ba.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Yadda fasinjoji suka hana jami'an tsaro kama El Rufai a filin jirgin sama
Ya kuma musanta cewa tsoro ne ya hana shi bin jami’an tsaron, inda ya ce:
“Ban tsoron komai sai Allah. Na yi shekaru da dama ina aikin gwamnati a ƙasar nan, kuma na sha ƙalubalantar duk wanda ke da wani zargi a kaina.
El-Rufa'i ya bayyana cewa ruwa ba zai taba kare masa ba a Najeriya saboda ya dogara ga Allah a kan dukkan abubuwan da suke faruwa.
Da aka tambaye shi ko ta kare masa sai El-Rufa'i ya ce:
"Yanzu ma ta fara, ai rigingimu da mai rai ake Madina. Sun san abin da zan iya yi, sun san zan iya kifar da su. Na fi jin karfin gwiwa idan ana irin rigingimun nan, kuma duk wanda ya ce kule, cas."

Source: Facebook
Ga bidiyon hirar da El-Rufa'i ya yi a kasa:
Za a kama Nasir El-Rufa'i
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa hukumomin Najeriya za su iya kama shi.
Malam Nasir El-Rufa'i ya bayyana haka ne a daidai lokacin da ya ke shirin dawowa Najeriya daga kasar Masar bayan wata tafiya.
Ya kara da cewa a yanzu haka an kama wasu daga cikin jami'an da suka yi aiki tare da shi a Kaduna, wanda hakan alama ce ta za a nemi shi.
Asali: Legit.ng