Mataimakin Gwamnan Kano Ya Aika Sako ga Majalisar Amurka kan Zargin da Ake Yi Wa Kwankwaso
- Ana ci gaba da magana kan yunkurin wasu 'yan majalisar dokokin Amurka na ganin an kakabawa Rabiu Musa Kwankwaso takunkumi
- Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya bayyana cewa Kwankwaso bai da tarihin muzgunawa mutanen da ba addininsu daya ba
- Gwarzo ya bukaci majalisar dokokin Amurka da ta cire sunan Kwankwaso daga cikin kudirin dokar da aka gabatar a gabanta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi magana kan yunkurin wasu 'yan majalisar Amurka na ganin an kakabawa Rabiu Musa Kwankwaso, takunkumi.
Aminu Abdulsalam Gwarzo ya bukaci majalisar dokokin Amurka da ta cire sunan tsohon gwamnan na jihar Kano daga kudirin dokar.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar a ranar Alhamis, 12 ga watan Fabrairun 2026.
Kudurin, wanda 'yan majalisar dokokin Amurka Riley Moore da Chris Smith suka dauki nauyi, yana neman sanya takunkumi ne ga wasu kungiyoyin Fulani, sannan ya hada da Kwankwaso a cikin jerin mutanen da ake zargi da keta hakkin addini.
Me mataimakin gwamnan Kano ya ce?
Aminu Abdulsalam ya bayyana cewa wadannan zarge-zarge ba su dace da tarihin rayuwa da hidimar Sanata Kwankwaso ya yi ga al’umma ba.
Ya bayyana cewa Kwankwaso ya yi wa Najeriya hidima a manyan mukamai daban-daban sama da shekaru 30.
Mukaman sun hada da mataimakin shugaban majalisar wakilai, gwamnan jihar Kano har sau biyu, Ministan tsaro, Sanata, sannan kuma dan takarar shugaban kasa a baya-bayan nan.
“Babu wani lokaci da aka taba samunsa da laifi, ko aka gurfanar da shi, ko kuma aka tuhume shi da kwakkwarar shaida kan gallaza wa addini, tsattsauran ra’ayi, ko keta hakkin bil’adama."
- Aminu Abdulsalam Gwarzo
Mataimakin Abba ya kare Kwankwaso
Ya bayyana cewa Kwankwaso ya dade yana adawa da tashe-tashen hankula, tsattsauran ra’ayi, da ta’addanci, jaridar Tribune ta kawo labarin.
Sanarwar ta kara bayyana yadda Kwankwaso ya yi mu’amala da shugabannin Kirista da kananan kabilu lokacin da yake kan mulki, sannan ta bayar da misali da takarar shugaban kasa ta 2023 da ya yi tare da Bishop Isaac Idahosa a matsayin shaida na kishinsa ga hadin kan addini da daidaiton kasa.

Kara karanta wannan
Da mamaki: Bulama ya ga kuskuren amurka kan zargin kwankwaso da matsawa kiristoci

Source: Facebook
Wane sako ya ba 'yan majalisar Amurka?
Mataimakin gwamnan ya yi kira ga ’yan majalisar dokokin Amurka da su yi watsi da shawarar baki daya kuma su cire sunan Kwankwaso daga kudurin dokar.
Ya yi gargadin cewa mai yiwuwa mutanen da ke da manufofin siyasa ko na kashin kai ne suka iza wutar wadannan zarge-zarge.
“Sanata Kwankwaso ya kasance mai kishin kasa, mai bin tafarkin dimokuradiyya, kuma babban jagora wanda hidimarsa ga al’umma ta ginu a kan adalci, hadin kai, da shugabanci na kowa da kowa."
- Aminu Abdulsalam Gwarzo
Ana son hana Kwankwaso zuwa Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin ana shiryawa Rabiu Musa Kwankwaso wata kullalliya.
Injiniya Buba Galadima ya yi zargin cewa jam'iyyar APC reshen jihar Kano na son hana Rabiu Musa Kwankwaso zuwa mahaifarsa.
Jagoran na NNPP ya bayyana cewa ana kokarin hana Kwankwaso zuwa garinsa ne saboda dalilai na siyasa, yana mai cewa hakan bai dace da tsarin doka da dimokuradiyya ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
