Otedola: Najeriya za Ta Ci Arzikin Dangote da Matatarsa Ta Tumbatsa wajen Tace Mai

Otedola: Najeriya za Ta Ci Arzikin Dangote da Matatarsa Ta Tumbatsa wajen Tace Mai

  • Matatar Dangote ta kai cikakken karfin tace mai na samar da ganga 650,000 a kowacce rana kamar yadda aka tsara da farko
  • Da wannan mataki da ta cimma, ana sa ran matatar za ta rika samar da Ana sa lita miliyan 75 na man fetur a cikin Najeriya
  • Fitaccen attajiri, Femi Otedola ya taya Dangote murna, ta fadi yadda 'yan Najeriya za su more wannan mataki na matatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos – Fitaccen ɗan kasuwa, Femi Otedola, ya taya Aliko Dangote murnar da matatarsa ta kai ƙarfin tace gangar mai 650,000 a rana.

Attajirin ya bayyana cewa wannan mataki da matatar Dangote ta kai, za ta taimaka wajen cicciba Najeriya da samun wadatar man fetur a kasa.

Kara karanta wannan

Gwamatin Tinubu ta gargadi matasa masu shiga soja a Rasha, ta gano yadda ake yi

Matatar Dangote ta kai matakin da aka gina ta a kai
Alhaji Aliko Dangote tare da Femi Otedola Hoto: Redefinition of self
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Otedola ya bayyana wannan ci gaba a matsayin wani sauyi mai girma ga Najeriya da ma nahiyar Afrika baki daya.

Femi Otedola ya jinjina wa Aliko Dangote

A sakon taya murna da ya fitar, Femi Otedola ya bayyana cewa wannan mataki da matatar Dangote ta kai abin farin ciki ne.

Otedola ya ce:

“Ina taya abokina kuma dan uwana, Aliko Dangote, murnar wannan gagarumar nasara da matatar Dangote ta kai cikakken karfin tace ganga 650,000 a rana.”
Matatar Dangote ta fara tace gangar mai N650,000 a kullum
Alhaji Aliko Dangote, Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

Ya kara da cewa:

“Abu mafi muhimmanci shi ne wannan sauyi ne ga Najeriya da Afrika. Samar da har lita miliyan 75 na man fetur a kullum yana sauya labarin makamashinmu tare da adana kudin musayar kasashen waje.”

Najeriya za ta amfana da Dangote - Otedola

'Dan kasuwar ya nuna cewa fara tace mai a cikin gida bayan shekaru masu yawa na dogaro da shigo da fetur daga waje zai rage matsin lamba a kasuwar musayar kudin waje.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta gano talakawan da suka fi bukatar taimako a Najeriya

Ya ce:

“Yanzu da aka fara tace mai a cikin gida bayan dogon lokaci na dogaro da shigo da kaya, matsin lamba a kasuwar musayar kudin waje zai ragu sosai.”

Otedola ya kuma bayyana yakinin cewa darajar Naira za ta kara karfi nan ba da jimawa ba sakamakon wannan ci gaba.

A cewarsa:

“Ina da kyakkyawan fata cewa Naira za ta kara karfi sosai, kuma za a iya rika ciniki a kasa da N1,000 ga kowacce Dala kafin karshen shekara.”

Yya bayyana cewa Dangote bai tsaya nan ba, domin ya fara wani karin zuba jari na Dala biliyan 12 domin kara karfin tace mai zuwa ganga miliyan 1.4 a rana.

An yi maraba da matatar Dangote

Muhammad Lawan, ɗaya ne daga cikin ƴan Najeriya masu shan mai kullum, ya shaida wa Legit cewa:

"Muna fata talaka ya samu Jin ga shikenan idan Naira ta sauko, farashin mai ya dai-daita,.komai zai yi sauki."

Kara karanta wannan

Bayan turo sojoji, Amurka za ta kafa 'tashar jiragen yaki' a a jihar Arewacin Najeriya

Dangote ya taso wani attajiri a gaba

A baya, mun wallafa cewa Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bai wa wani fitaccen dan kasuwa a jihar Kaduna, Kailani Mohammed wa'adin shiga taitayinsa.

Alhaji Aliko Dangote ya bai Alhaji Kailani Mohammed wa’adin kwana bakwai domin ya janye kalaman da ake zargin sun bata masa suna ko a dauki mataki a kansa.

Rahotanni sun nuna cewa Dangote ya bukaci dan kasuwar ya ba da hakuri a bainar jama’a cikin wa’adin da aka kayyade, ko kuma ya fuskanci matakin shari’a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng