Bidiyo: Yadda Fasinjoji Suka Hana Jami'an Tsaro Kama El Rufai a Filin Jirgin sama
- Jami'an tsaro sun yi yunkurin kama tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai a filin jirgin Abuja yau bayan ya dawo daga Cairo
- An rahoto cewa fasinjoji da magoya baya sun hana jami'an tsaron tafiya da tsohon gwamnan, amma an kwace fasfonsa
- Nasir El-Rufai ya kalubalanci jami'an tsaron da su mika masa takardar gayyata maimakon su yi kokarin kama shi ta karfin tsiya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A yau Alhamis, 12 ga Fabrairu, 2026, jami'an tsaro suka yi yunkurin kama tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai a filin jirgin sama.
An rahoto cewa, jami'an tsaron sun yi wannan yunkuri ne lokacin da El-Rufai ya sauka daga kan jirgi, bayan ya dawo Najeriya daga kasar Cairo.

Source: Twitter
Fasinjoji sun hana a kama El-Rufai
Wani bidiyo da Isiyaka Aliyu ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya nuna lokacin da dandazon mutane suke kokarin fitar da El-Rufai daga filin jirgin.

Kara karanta wannan
Jami'an tsaro sun ga takansu da suka yi yunkurin kama El Rufai a filin jirgin sama
Isiyaka ya wallafa cewa:
"'Yanda fassinjoji suka hana hukuma kama Malam Nasir El-Rufa’i a filin jirgin sama dake Abuja, duk da sun yi nasarar kwace fasfonsa."
A cikin bidiyon, an ji wani na cewa:
"Ba wanda ya isa, sai ya je gida. Shi shugabanmu ne, babu abin da zai faru."
Filin jirgin ya cika da masu kallo a lokacin da ake kokarin hana jami'an tsaro kama El-Rufai, kuma da alama, an yi nasara kan hakan.
Sai dai, Legit Hausa ba ta iya tantance ko dukkan mutanen da aka gani a cikin bidiyon fasinjoji ne ko har da masu tarbar tsohon gwamnan ba.
Kalli bidiyon a kasa:

Source: Twitter
"Ku kawo mun takardar gayyata" - El-Rufai
A filin jirgin, an ga Malam Nasir El-Rufai yana magana da wani jami'in tsaro, wanda ake kyautata zaton yana a tawagar masu yunkurin kama tsohon gwamnan.
A cikin bidiyon, wanda mai tallafawa shugaban APC na kasa kan kafofin sada zumunta, Imran Muhammad ya wallafa a shafinsa na X, an ji El-Rufai yana fadawa jami'in cewa:
"Ka ji ni da kyau, babu wanda ya isa, kai hatta shugaban kasa bai isa ya ce sai na yi 'kaza' ba. Idan kuna son gayyata ta, to ku rubuta mun takarda, shi ne kawai."
Kalli bidiyon a nan kasa:
El-Rufai zai mika kansa ga EFCC
Tun da fari, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya shiya dawowa gida Najeriya kuma zai mika kansa ga EFCC.
Wannan mataki ya saba wa raɗe-raɗin da ake yi na cewa tsohon gwamnan ya yi gudun hijira ne sakamakon takaddama tsakaninsa da gwamnatin tarayya.
El-Rufai ya fita ƙasar waje ne a ranar 30 ga Nuwamba, 2025, bayan ya halarci wasu tarukan liyafa a birnin Legas kwana ɗaya kafin tafiyarsa.
Asali: Legit.ng
