Jami'an Tsaro Sun ga Takansu da Suka Yi Yunkurin Kama El Rufai a Filin Jirgin Sama
- Rahotanni sun tabbatar da cewa tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya gamu da jami'an tsaro a filin jirgin sama na Abuja
- Jami'an tsaron sun yi yunkurin kama El-Rufai amma ya ce ba zai bi su ba saboda babu takardar gayyata a hukumance
- Babu wata sanarwa a hukumance daga hukumomin tsaron Najeriya, amma an ce jami'an sun kwace fasfon tsohon gwamnan
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Rahotanni da ke shigo mana sun bayyana cewa jami’an tsaro sun yi yunƙurin kama tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a Abuja.
An ruwaito cewa dakarun tsaron sun yi wannan yunkuri ne yayin da ya El-Rufai ya sauka Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja daga birnin Cairo na ƙasar Masar.

Source: Twitter
Zargin ya fito ne daga mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na X jim kaɗan bayan faruwar lamarin.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Yadda fasinjoji suka hana jami'an tsaro kama El Rufai a filin jirgin sama
El-Rufai ya ci karo da jami'an tsaro a Abuja
A cewar Adekeye, jami’an tsaron sun tunkari El-Rufai ne bayan ya sauka daga jirgin da ya dawo da shi Najeriya, inda suka nemi su tafi da shi domin tsarewa.
Sai dai ya ce tsohon gwamnan ya ƙi bin su, yana mai cewa ba zai amsa wannan buƙata ba sai an ba shi gayyata ko sammaci a hukumance.
Sanarwar ta ce:
“A yau jami’an tsaro sun yi yunƙurin kama Malam Nasir El-Rufai yayin da ya iso gida Najeriya daga Cairo. Malam El-Rufai ya ƙi bin su saboda ba a ba shi takardar gayyata a hukumance ba.”
An kwace fasfon El-Rufai a filin jirgi
Adekeye ya kuma yi zargin cewa jami’an tsaron sun ƙwace fasfon El-Rufai a yayin arangamar da ta faru a filin jirgin sama na Abuja.
“Sai dai sun ƙwace fasfonsa daga hannun wani hadiminsa,” in ji shi.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga hukumomin tsaro da ta tabbatar ko musanta wannan zargi.
Har yanzu ba a bayyana ko Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ko Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC) ce ke da hannu a yunƙurin kama Malam Nasir El-Rufai ba.

Source: Twitter
El-Rufai ya gano shirin kama shi
Amma a wata hira da ya yi da BBC Hausa a baya-bayan nan, El-Rufai ya bayyana cewa da yiwuwar jami'an tsaro su kama kwanan nan.
El-Rufai, wanda jigo ne a jam’iyyar adawa ta ADC ya kuma yi zargin cewa ana amfani da matsin lambar siyasa wajen tilasta wa wasu ‘yan siyasa sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
El-Rufai ya sake dura kan gwamnatin Tinubu
A baya, kun ji cewa Malam Nasiru El-Rufai ya yi zargin cewa gwamnatin Bola Tinubu na iya amfani da kafar da aka ba da a dokar zabe wajen tafka magudi a zaben 2027.
Tsohon gwamnan ya ce damar da aka ba da ta rubuta sakamakon zabe a inda babu intanet, ya ba da kafar da za a iya yin magudi kafin zuwa cibiyoyin tattara sakamako.
Ya yi ikirarin cewa idan da gaske ake yi, za a iya tura sakamakon zabe ta intanet daga kowace rumfa a fadin Najeriya.
Asali: Legit.ng
