Buba Galadima Ya Fadi Dalilin Yi wa Kwankwaso Bita da Kulli a Kasar Amurka

Buba Galadima Ya Fadi Dalilin Yi wa Kwankwaso Bita da Kulli a Kasar Amurka

  • Babba a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya ce gyaran dokar zaɓe da aka yi bata cika ka’ida ba, ya zargi majalisa da bin hanya maras dorewa
  • Ya bayyana cewa zargin da ake yi wa Sanata Rabiu Kwankwaso da alaƙa da tallafa wa ta’addanci a matsayin makarkashiyar siyasa
  • Dan siyasar ya jaddada cewa Kwankwaso ya taɓa rasa zaɓe saboda tsayawa kan akidarsa, yana mai cewa har yanzu yana da tasiri a siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Jagora a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi Allah-wadai da batun gyara dokar zaɓen Najeriya, tare da kare ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Rabiu Musa Kwankwaso daga zargi.

Buba Galadima ya bayyana cewa zargin da ake yi wa Rabiu Kwankwaso ba shi da tushe, yana mai danganta shi da kulle-kullen siyasa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana daga India ana caccaka tsinke da Amurka

Jigon NNPP, Buba Galadima
Buba Galadima yana magana a taron NNPP. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

Ya yi bayani ne a wata hira da ya yi da tashar Arise News, inda ya yi martani kan zargin da 'yan majalisar wakilan Amurka suka danganta Kwankwaso da tallafa wa ta’addanci.

Suka kan gyaran dokar zaɓen Najeriya

Da yake magana kan matsayar majalisar dattawa game da tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo, Buba Galadima ya ce ‘yan majalisar ba su yi wani sahihin gyara ga dokar zaɓen 2022 ba.

A cewarsa:

“Ba su yi wani gyara a dokar zaɓe ta 2022 ba domin sun bar ta yadda take. Abin da suka yi kawai shi ne yi wa 'yan kasa wayau. Kuma suna tunanin kowa kurma ne, bebe ne kuma marar hankali kamar su.”

Ya nuna cewa matakin da aka ɗauka bai warware matsalolin da ake fuskanta ba, yana mai zargin cewa an yi sauyin ba tare da cikakken tsari ba.

Kara karanta wannan

APC ta ajiye bambanci, ta shiga wa Kwankwaso fada da Amurka

Buba Galadima ya kare Kwankwaso

Da aka juya kan batun zargin da aka yi wa Rabiu Kwankwaso a kasar Amurka, Buba Galadima ya bayyana shi a matsayin rashin adalci.

Ya ce:

“Ina ganin wannan abu ne mafi rashin adalci. Rashin adalci ga Kwankwaso, ga mutuncinsa, da kuma ga martabarsa a matsayin ɗan Najeriya mai son zaman lafiya.
"Abin da mu ke gani shi ne makirce-makircen zaɓen 2027.”

Ya yi watsi da iƙirarin cewa Kwankwaso ya tallafa wa ta’addanci, yana mai cewa tarihin siyasarsa a Kano ya nuna tsayuwa kan akida da bin ka’ida.

Rabiu Musa Kwankwaso a taro
Rabiu Musa Kwankwaso tare da wasu 'yan NNPP a Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Buba Galadima ya tuna cewa Kwankwaso ya tsaya tsayin-daka kan ra’ayinsa duk da cewa hakan ya jawo masa faduwa zaɓe a lokacin da ya ke neman tazarce a Kano.

Ya kuma jaddada cewa a lokacin aiwatar da Shari’a, Kwankwaso ya nuna taka-tsantsan kuma shi ne na ƙarshe cikin gwamnonin Najeriya da suka aiwatar da ita.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fita kasar waje, ya yi magana kan sauya shekar Abba Kabir

Ga bidiyon da Buba Galadima ya yi magana a kasa:

Kwankwaso: An tura wasika ga Majalisar Amurka

A wani labarin, kun ji cewa Fasto Isaac Idahosa da ya yi takara tare da Sanata Rabiu Kwankwaso ya tura wasika ga majalisar dokokin Amurka.

Faston ya bayyana cewa akwai bukatar a sake bincike game da Rabiu Kwankwaso lura da cewa zargin da aka yi ya saba da halinsa.

Ya bukaci majalisar Amurka ta janye sunan Sanata Rabiu Kwankwaso cikin wadanda ake neman a kakaba musu takunkumi da hana biza.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng