Da Mamaki: Bulama Ya ga Kuskuren Amurka kan Zargin Kwankwaso da Matsawa Kiristoci
- Fitaccen lauya, Barista Audu Bulama Bukarti ya bayyana mamakin hango sunan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a cikin kudirin majalisar Amurka
- A makon nan Riley Moore, 'dan majalisar Amurka ya ce sun gabatar da kuduri a gaban zaurensu domin duba a kan zargin muzgunawa kiristocin Najeriya
- A cikin kudurin, an nemi Amurka ta hukunta wasu fitattun Najeriya da suka hada da Sanata Kwankwaso da kungiyoyin Fulani Makiyaya a kasar nan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Lauya kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Audu Bulama Bukarti, ya soki saka sunan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a cikin wani kudirin majalisar Amurka.
'Yan majalisar sun gabatar da kudiri a Majalisar Wakilan Amurka, wanda ke neman kakaba takunkumi kan wasu mutane.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Bulama Bukarti ya bayyana cewa, a yi maganar gaskiya, babu ruwan Kwankwaso da tsaurin addini.
Bulama Bukarti ya kalubalanci 'yan majalisar Amurka
A rubutunsa, Bukarti ya ce ya kamata a janye sunan Kwankwaso daga kudirin ba tare da bata lokaci ba.
Ya kara da cewa wannan lamari ya fito da irin raunin bayanan da ake amfani da su wajen yada labarin wai ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.
A cewarsa, masu yada wannan batu suna kirkirar zarge-zarge marasa tushe ne, sannan su rika komawa kan wadannan zarge-zarge a matsayin hujja.
Ya nuna cewa irin wannan hanya ba ta dace a yi amfani da ita a wajen yanke hukunci a kan al'amurand a suka shafi kasashe da mutanensu ba.
Martanin jama’a ga 'yan majalisar dokokin Amurka
Maganar ta haifar da martani daga jama’a, musamman a kafafen sada zumunta da ke ganin 'yan majalisar Amurka sun yi kuskure.

Source: Facebook
Babangida Galadima ya ce:
“Wannan batu ne na shekarar 2031. Remi na yin fafutuka saboda yaronta a siyasa Nuhu Ribadu, tana yi masa sharar fage domin ya zama Shugaban kasa.Kwankwaso na daga cikin wadanda za su iya kawo cikas a wannan lokaci."
Nasir Hassan Aliyu ya goyi bayan Bukarti inda ya ce:
"Sanya sunan Kwankwaso shi kadai a cikin wannan jerin wadanda ake tuhuma ba tare da cikakke kuma gamshashen bayani ba, ya diga alamar tambaya a kan zargi da suke kokarin kakaba wa."
ku Mai Bakin Magana ya ce:
"Kwankwaso dodar a shekarar 2027, shi ne zabinmu."
Amurka: Wasu kiristoci sun kare Kwankwaso
A baya, mun wallafa cewa wasu fitattun ‘yan Najeriya, daga ciki har da Kiristoci daga jihar Kano, sun fito kare tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Sun wanke shi daga kan zargin da wani kwamitin Majalisar Dokokin Amurka ya yi tare da tsoma sunansa cikin jerin mutanen da ake zargi da hannu a muzgunawa Kiristoci.
Rahotanni sun nuna kwamitin ya aike da wani kudirin doka da ke neman a sanya sunan Sanata Kwankwaso cikin jerin mutanen da za a kakaba wa takunkumi a kan zargin kisan kiristoci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

