El Rufai Zai Mika Kansa ga Hukumar EFCC, Ya Sanya Ranar da Zai Dawo Najeriya
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai zai dawo Najeriya nan da kwanaki biyu domin amsa gayyatar hukumar EFCC
- El-Rufai ya musanta rade-radin cewa ya gudu kasar waje ne domin ya tsere wa binciken cin hanci da rashawa da ake masa
- A tattaunawa da manema labarai, El-Rufai ya bayyana ranar da zai je ofishin EFFC, inda har ya ce ba makawa za a kama shi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - An tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai zai dawo gida Najeriya domin amsa kiran hukumar EFCC.
Wannan mataki ya saba wa raɗe-raɗin da ake yi na cewa tsohon gwamnan ya yi gudun hijira ne sakamakon takaddama tsakaninsa da gwamnatin tarayya.

Source: Twitter
Nasir El-Rufai ya shirya dawo wa Najeriya
Jaridar Premium Times ta tabbatar da cewa El-Rufai yana shirin dawowa nan da sa'o'i 48, kuma ya sanar da EFCC cewa zai bayyana a ofishinsu ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, 2026.
"Zan dawo gida Najeriya nan ba da jimawa ba," in ji Nasir El-Rufai yayin da yake tabbatar da wannan labari a wata gajeriyar tattaunawa da ya yi.
El-Rufai ya fita ƙasar waje ne a ranar 30 ga Nuwamba, 2025, bayan ya halarci wasu tarukan liyafa a birnin Legas kwana ɗaya kafin tafiyarsa.
EFCC ta aika wasika gidan El Rufai
Yayin da yake a ƙasar, hukumar EFCC ta aika da takardar gayyata zuwa gidansa a watan Disamba na shekarar 2025, wanda hakan ya jawo raɗe-raɗin cewa za a iya kama shi.
Tun bayan barinsa ofis a shekarar 2023, labaran tsohon gwamnan Kaduna sun ci gaba da jan hankalin jama'a, musamman dangane da irin rawar da ya taka a siyasar ƙasar.
Rahoto ya nuna cewa Nasir El-Rufai ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin Shugaba Bola Tinubu ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a zaɓen 2023.
Sabani tsakanin El-Rufai da Tinubu
Duk da irin goyon bayan da ya ba shugaban ƙasa, majalisar dattawa ta ƙi amincewa da naɗin El-Rufai a matsayin minista sakamakon wasu rahotannin tsaro, in ji rahoton Legit Hausa.
Bayan wannan lamari, El-Rufai ya janye jikinsa, inda daga bisani alaƙarsa da Tinubu ta yi tsami har ya fita daga jam’iyyar APC zuwa ADC.
A yanzu, El-Rufai ya zama ɗaya daga cikin masu sukan manufofin Shugaba Tinubu, wanda hakan ke ƙara zafi a fagen siyasar Najeriya.

Source: Twitter
Binciken EFCC da zargin cin hanci
A halin yanzu, hukumomin EFCC da ICPC suna gudanar da bincike kan zarge-zargen cin hanci da rashawa da suka shafi lokacin mulkinsa, in ji rahoton BusinessDay.
Tsohon gwamnan ya musanta dukkan zarge-zargen, inda yake ikirarin cewa bita-da-ƙulli kawai ake yi masa saboda matsayarsa ta siyasa.
Jama'a na dakon ganin yadda wannan ziyara ta El-Rufai zuwa ofishin EFCC za ta kasance a ranar Litinin mai zuwa, 16 ga Fabrairu, 2026.
"Za a kama ni" - Nasir El-Rufai
A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa'i ya yi maganar da ke nuna cewa zai iya shiga hannun hukumomin Najeriya.
El-Rufai wanda yana ketare ya bayyana haka ne lura da yadda aka kama wasu daga cikin wadanda suka yi aiki da shi a lokacin da ya ke gwamna a Kaduna.
Tsohon gwamnan ya ce duk da har yanzu ba a kama shi ba, amma an kama wasu na kusa da shi, lamarin da ya sa yake ganin shi ma ana iya zuwa kansa nan gaba kadan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

