Takunkumin Amurka: Yadda Kwankwaso Ya Kira Sunan Trump Ya Caccake Shi
- 'Yan Najeriya na cigaba da tofa albarkacin baki game da barazanar da wasu 'yan majalisar Amurka suka fara yi wa Rabiu Musa Kwankwaso
- A watan Disamban 2025 Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi martani kai tsaye ga shugaban Amurka, Donald Trump kan matsalar tsaron Najeriya
- Masana sun yi karin bayani game da alakar maganar Rabiu Kwankwaso kan Donald Trump da bukatar kakaba wa masa takunkumi da ake
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Masana sun fara sharhi kan alakar wasu maganganu da Rabiu Kwankwaso ya yi a baya da barazanar da 'yan majalisar Amurka suka fara masa.
Wasu 'yan majalisar dokokin kasar Amurka sun bukaci a sakawa Rabiu Kwankwaso da wasu kungiyoyin Fulani takunkumi kan zargin tauye hakkin addini.

Kara karanta wannan
Jaafar Jaafar ya ja hankalin Amurka, ya nuna shaidar da Kiristoci suka yi wa Kwankwaso

Source: Facebook
Mun tattaro muku martanin da Kwankwaso ya yi wa Shugaban Amurka, Donald Trump kai tsaye a 2025 a shafinsa na Facebook game da tsaron Najeriya.
Maganar Kwankwaso kan Trump
A lokacin da shugaban Amurka ya zafafa harshe game da Najeriya a kan tsaro da zargin kisan Kiristoci, Sanata Kwankwaso ya fito ya ce:
"Na lura da ƙara tsananta furucin da Shugaba Donald Trump ke yi kan Najeriya, lamarin da ya biyo bayan ayyana Najeriya a matsayin “ƙasa mai matuƙar damuwa ta musamman.”
"Yana da muhimmanci a jaddada cewa ƙasarmu ƙasa ce mai cikakken ‘yanci, kuma al’ummarta na fuskantar barazana iri-iri daga masu aikata laifi a sassa daban-daban. Rashin tsaron da muke fuskanta ba wani addini tilo ya shafa ba."
"Ya dace Amurka ta tallafa wa hukumomin Najeriya da ingantacciyar fasaha ta zamani domin tunkarar waɗannan matsaloli, maimakon ɗaukar matakan da ka iya ƙara raba kan al’ummarmu."
Kwankwaso ya kara da cewa:
"Ya kamata gwamnatin Najeriya ta tura wakilai na musamman daga cikin gogaggun jami’an diflomasiyyarta domin tattaunawa da gwamnatin Amurka.
"Haka kuma, akwai buƙatar naɗa jakadu na dindindin domin wakiltar muradun Najeriya a fagagen ƙasa da ƙasa."
Me ya harzuka Amurka kan Kwankwaso?
Wani 'dan Najeriya da ke zaune a Amurka kuma mai sharhi kan lamuran yau da kullum, Farfesa Faruq Kperogi ya ce martanin da Kwankwaso ya yi ne ya harzuka 'yan majalisar Amurka.
Kperogi wanda Farfesa ne a bangaren harshen Ingilishi da aikin jarida ya wallafa a Facebook cewa:
"To me ya sa Riley Moore da abokan aikinsa suka ware shi (Kwankwaso) kaɗai?
"Amsar a bayyane take. Kwankwaso ne kaɗai babban ɗan siyasar Najeriya da ya fito fili ya soki ayyana Najeriya da Amurka ta yi a matsayin kasa mai bukatar kulawa."

Source: Facebook
Amurka: Jam'iyyar APC ta kare Kwankwaso
A wani labarin, kun ji cewa Sakataren yada labaran jam'iyyar APC na kasa, Bala Ibrahim ya soki Amurka kan barazanar da ta fara yi wa Rabiu Kwankwso.
Bala Ibrahim ya ce bai kamata kasa kamar Amurka ta ce za ta dauki mataki a kan mutum irin Kwankwaso bisa rade-radi da zargi ba tare da hujja ba.
APC ta bukaci 'yan majalisar Amurka da suka mika bukatar da su girmama tsarin dimokuradiyya da suka dade suna kira gare shi a tarihi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

