Fulani Makiyaya Sun Fara Buga wa da Amurka kan Saka Takunkumi
- Kungiyar Fulani makiyaya ta MACBAN ta ce ta yi mamakin yadda Majalisar dokokin Amurka ke shirin ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci ba
- Shugaban ƙungiyar, Baba Othman, ya bayyana matakin a matsayin rashin adalci da zai iya bata sunan ƙungiyar a Najeriya da duniya baki daya
- Hakan na zuwa ne bayan 'yan majalisar sun ba da shawarar ƙaƙaba takunkumi kan kungiyar da wasu mutane bisa zargin take hakkin Kiristoci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar Fulani makiyaya ta MACBAN ta yi watsi da matakin da majalisar dokokin Amurka ta ɗauka na neman ayyana ta a matsayin 'yar ta’adda.
Kungiyar ta bayyana cewa ba ta taɓa shiga harkar laifi ko tallafa wa wata ƙungiyar ta’addanci ba tun bayan kafuwarta shekaru 42 da suka wuce a Najeriya.

Source: Facebook
Shugaban ƙungiyar, Baba Othman ya shaida wa jaridar the Sun cewa sun yi mamakin yadda aka ɗauki irin wannan mataki ba tare cikakken bincike ba.
Ta'addanci: Martanin Fulani ga Amurka
Da yake karin haske, Baba Othman ya ce ya karanta rahoton da aka fitar, inda ya bayyana mamakinsa kan abin da ya kira rashin adalci daga ‘yan majalisar dokokin Amurka.
Ya ce:
“Na karanta rahoton tun da safe, kuma na yi mamakin ganin irin wannan mu’amala marar adalci daga ‘yan majalisar Amurka. Wannan kiran mu da ƙungiyar ta’addanci abu ne da ba mu taɓa ji ko sani ba.
"MACBAN ƙungiya ce da ta shafe shekaru 42 tana aiki a Najeriya bisa doka, ba tare da shiga harkar laifi ko tallafa wa wata ƙungiyar masu laifi ko ta’addanci ba.”
Kungiyar MACBAN na kula da makiyaya
Ya ƙara da cewa MACBAN ita ce babbar ƙungiyar da ke wakiltar duk makiyaya a faɗin Najeriya ba tare da la’akari da bambancin addini, siyasa, ƙabila ko zamantakewa ba.
A cewar shugaban, duk wanda makiyayi ne kuma ya yi rijista da su, ƙungiyar na kula da muradunsa tare da kare haƙƙinsa.
Ya jaddada cewa a tsawon shekarun da suka yi suna aiki a ƙasar, ba a taɓa danganta su da wata ƙungiyar ta’addanci ko mutane masu hannu a ayyukan laifi ba.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto Baba Othman ya ce yana mamakin yadda gwamnatin Amurka za ta ɗauki irin wannan mataki a kan ƙungiya da ya bayyana a matsayin mai son zaman lafiya.
Kiran Fulani ga gwamnatin Najeriya
Baba Othman ya ce ƙungiyar za ta tuntuɓi Gwamnatin Tarayya domin neman kariyar diflomasiyya da kuma ɗaukar matakan da za su taimaka wajen soke matakin majalisar dokokin Amurka.
Ya ce:
“Ba za mu iya shiga takaddama da gwamnatin Amurka ba. Amma abin da ya fi dacewa gare mu shi ne mu tuntuɓi Gwamnatin Tarayya, wadda ƙarƙashinta muka shafe shekaru 42 muna aiki tare da biyan dukkan harajin da ya dace."
Kwankwaso: Martanin APC ga 'yan majalisar Amurka
A wani labarin, mun kawo muku cewa jam'iyyar APC mai mulki ta yi wa Amurka raddi game da shirin sakawa Rabiu Musa Kwankwaso takunkumi.
Sakataren yada labaran APC, Bala Ibrahim ya bayyana cewa ba su yarda da matakin da Amurka ke shirin dauka game da Kwankwaso ba.
Bala Ibrahim ya kara da cewa bai kamata Amurka ta dauki irin wannan matakin ba tare da bincike da ba wanda ake zargi damar kare kan shi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


