APC Ta Ajiye Bambanci, Ta Shiga wa Kwankwaso Fada da Amurka

APC Ta Ajiye Bambanci, Ta Shiga wa Kwankwaso Fada da Amurka

  • Shirin da wasu 'yan majalisar Amurka suka fara na sanyawa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso takunkumi na cigaba da daukar hankali a Najeriya
  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta nuna damuwa kan batun tare da kira da cewa a bar komai a bayyane domin a yi wa Kwankwso adalci
  • APC ta kara da cewa zargi kadai da ake yi wa jagoran NNPP bai kai a sanya masa takunkumi ba, tana cewa bai kamata a tauye masa hakki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta yi watsi da shirin hana bayar da biza da rike kadarori da wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka suka ba da shawara a kan tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Jaafar Jaafar ya ja hankalin Amurka, ya nuna shaidar da Kiristoci suka yi wa Kwankwaso

Haka zalika 'yan majalisar na so matakin ya shafi ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah da kuma Miyetti Allah Kautal bisa zargin take hakkin ‘yancin addini a Najeriya.

Jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a taron 'yan Kwankwasiyya. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa dan majalisar wakilan Amurka Chris Smith ne ya gabatar da kudirin tare da abokan aikinsa Riley Moore, Brian Mast da Bill Huizenga.

Abin da Amurka ke so kan Rabiu Kwankwaso

Kudirin 'yan majalisar ya ba da shawarar kakaba takunkumin hana biza da rike kadarori ƙarƙashin dokar hakkin dan Adam ta GMHRAA.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Amurka ta wallafa cewa dokokin GMHRAA suna shafar daidaikun mutane da ƙungiyoyi da ake zargi da hannu a take hakkin ‘yancin addini.

Kwankwaso: Martanin APC ga 'yan majalisar Amurka

APC ta soki shirin takunkumin, tana mai jaddada cewa zargi kaɗai ba zai zama hujjar tauye wa Kwankwaso ‘yancin zirga-zirga ba tare da an ba shi damar kare kansa ba bisa ƙa’ida da tsarin shari’a.

Daraktan yaɗa labarai na APC, Bala Ibrahim, ya bayyana Amurka a matsayin ƙasar da ta shahara da dimokuraɗiyya, inda ya ja hankalin gwamnatin ƙasar da kada ta ɗauki mataki bisa zargi kaɗai.

Kara karanta wannan

Zargin kashe kiristoci: Amurka ta taso Kwankwaso da ƙungiyoyin Fulani a gaba

Ya ce:

“Ina ganin su (Amurka) ba za su ɗauki mataki bisa zargi kawai ba. Amurka ita ce abar koyi a fannin dimokuraɗiyya. Amurka ita ce abar koyi a fannin ‘yanci, kuma ya kamata a gan ta tana tafiya a kan wannan tafarki.
“Yanzu, duk wani zargi da ake yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da wasu, zargi ne har sai an tabbatar da shi.
“Bai kamata saboda zargi kawai ba su ba da shawarar hanawa ko takaita ‘yancin zirga-zirgar mutum ba tare da sun gabatar da hujja ba, ba tare da ba shi damar kare kansa a gaban shari’a ba.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump
Donald Trump yayin wani taro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kwankwaso: Martanin NNPP ga Amurka

A wani labarin, kun ji cewa NNPP ta bayyana shirin takunkumi ga jagoranta na ƙasa, Rabiu Kwankwaso a matsayin yunƙurin matsa lamba da kuma batanci.

Jam’iyyar adawar ta nuna mamaki kan saka sunan Kwankwaso cikin jerin sunayen da ake shirin kakaba wa takunkumi a Amurka, tare da yin watsi da duk wata magana da ke danganta da ta'addanci.

Kakakin NNPP, Ladipo Johnson ya ce suna kallon wannan lamari a matsayin wani shiri da aka kitsa a kan mutum marar laifi da ba shi da alaƙa da tsattsauran ra’ayi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng