'Daga Allah ne': Fasto Ya Gina Makeken Masallaci, Ya Tabo Batun Shiga Musulunci

'Daga Allah ne': Fasto Ya Gina Makeken Masallaci, Ya Tabo Batun Shiga Musulunci

  • Shugaban cocin 'INRI Evangelical Spiritual', Fasto Elijah Ayodele, zai kaddamar da sabon masallaci da ya gina
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa babban limamin Kiristan ya gina masallacin shi kadai ba tare da taimakon kowa ba
  • Ya ce ginin masallacin umarni ne daga Allah, ba wai yana son sauya addini ba ne, domin yana da kyakkyawar alaka da Musulmi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban cocin 'INRI Evangelical Spiritual', Fasto Elijah Ayodele zai kaddamar da masallacin da ya gina.

Faston ya tabbatar da cewa ya kammala shirye-shiryen kaddamar da sabon masallacin da ya gina shi kaɗai a ranar Asabar, 14 ga watan Fabrairu, 2026.

Fasto zai kaddamar da babban masallaci da ya gina
Fasto Elijah Ayodele wanda ya gina masallaci. Hoto: Primate Elijah Ayodele.
Source: Twitter

Yaushe faston zai kaddamar da bude masallaci?

Za a gudanar da bikin kaddamarwar ne a cikin kwanaki 21 da ya ware domin yabo da yin godiya da ya saba duk shekara, wanda ya fara a watan Janairu kuma zai kare a ranar Lahadi, 15 ga Fabrairu, 2026, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun riƙewa minista wuta a kan 'bacewar' kayan Gwamnatin Tarayya

A cewarsa, shawarar gina masallacin ba wai saboda yana son sauya addininsa ba ne, sai dai domin bin umarnin da Allah ya ba shi tun shekaru da dama da suka gabata.

Ya bayyana cewa cocinsa ta kasance mafaka ga Musulmi, kuma sau da dama ana gayyatarsa domin yin wa’azi a tarukan Musulmi daban-daban.

Saboda haka, gina masallaci bai kasance abu mai wahala ba a gare shi, musamman bayan ya samu umarnin Allah kan lamarin.

Ya ce:

“Shawarata ta gina masallaci ba don in zama Musulmi ba ne, amma wakilcin abin da Allah ya umurce ni in yi ne.
“Ina da Musulmi da ke halartar cocina, ni ma ina halartar shirye-shiryen Musulmi idan an gayyace ni domin yin wa’azi, kuma ina da abokai Musulmi da dama.
“Saboda haka, bin umarnin da Allah ya ba ni bai kasance abu mai wahala ba a gare ni.”
Fasto ya kawar da jita-jitar shiga Musulunci
Babban Fasto a Najeriya, Elijah Ayodele tare da mabiyansa. Hoto: Primate Elijah Ayodele.
Source: Facebook

Dalilin gina masallacin da Fasto ya yi

Fasto Ayodele ya kuma ce gina masallaci a matsayinsa na fasto na Kirista na isar da sakon hakuri da juna a tsakanin addinai a duniya baki daya.

Kara karanta wannan

Sanata ya shawarci Musulmi kan yadda za su kalubalanci malamai

Ya kara da cewa idan aka warware matsalar rikicin addini a duniya, lallai duniya za ta zama wuri mafi alheri ga kowa, cewar rahoton PM News.

Ya ce yana kaunar kowa ba tare da la’akari da addini ko kabila ba, kuma gina masallaci na kara nuna wannan kaunar da yake yi wa bil’adama.

Game da yadda za a tafiyar da masallacin, ya bayyana cewa za a mika shi gaba daya ga al’ummar Musulmi ba tare da wani tsoma baki daga bangarensa ba.

Ya kara da cewa, da yardar Allah, za a sanya wa masallacin sunan marigayiyar mahaifiyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu kafin a mika shi ga Musulmai domin su kula da shi yadda ya kamata.

Fasto ya sake gargadin Tinubu kan gwamnoni

An ji cewa fitaccen limamin coci a Najeriya, Fasto Elijah Ayodele, ya yi hasashen wahalar da Shugaba Bola Tinubu zai fuskanta a zaben 2027.

Ayodele ya yi ikirarin cewa ya hango wasu gwamnoni takwas a APC da ba za su marawa kudirin tazarcen Shugaba Tinubu baya ba

Ya kuma bayyana cewa akwai wani babban kusa a siyasar Najeriya da zai sauya sheka zuwa jam'iyyar hadaka, ADC nan ba da jimawa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.