Ana Wata ga Wata: Tinubu na Shirin Sayar da Manyan Kadarorin Najeriya

Ana Wata ga Wata: Tinubu na Shirin Sayar da Manyan Kadarorin Najeriya

  • Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara shirin fara sayar da wasu kadarorin gwamnati domin kara habaka jari
  • Ministan Kudi, Wale Edun, ya ce ana tantance kadarorin da za a sayar tare da tsara jadawalin lokacin sayar da su ga 'yan kasuwa
  • Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce sauye-sauyen tattalin arziki da aka yi sun kara wa Najeriya kima a idon masu zuba jari

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja Gwamnatin Najeriya ta bayyana aniyarta ta fara sayar da wasu kadarorin gwamnati ga masu zuba jari da 'yan kasuwa a 2026, a wani yunkuri na kara jawo kasashen waje cikin gida.

Ministan Kudi, Wale Edun, ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin wata hira da aka yi da shi a taron AlUla kan tattalin arzikin kasashe masu tasowa da aka gudanar a kasar Saudiyya.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun riƙewa minista wuta a kan 'bacewar' kayan Gwamnatin Tarayya

Ministan kudin Najeriya, Wale Edun
Ministan kudi na Najeriya, Wale Edun na bayani a wani taro. Hoto: Federal Ministry of Finance
Source: Facebook

Rahoton Bloomberg ya ce gwamnati na kan aikin tantance irin kadarorin da za a sayar tare da tsara jadawalin lokacin da za a mika su ga masu zuba jari.

Najeriya za ta sayar da kadarorinta

Wale Edun ya ce gwamnati na shirin fara sayar da wasu kadarori a shekarar 2026, yana mai cewa an riga an fara shirye-shiryen da suka dace.

Tun bayan hawansa mulki a watan Mayu, 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da jerin sauye-sauye a fannin tattalin arziki.

A cewar Edun, wadannan matakai sun taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyaki, daidaita darajar Naira tare da kara kudin shiga.

Najeriya za ta hada kai da 'yan kasuwa

Najeriya, wadda ita ce babbar mai fitar da danyen mai a Afirka, ta sanar da cewa tana tattaunawa da wani kamfani daga kasar China da wasu masu zuba jari kan yadda za su tafiyar da wasu matatun man gwamnati.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Bayan turo sojoji, an hango abin da Amurka za ta yi a zaben Najeriya na 2027

Rahotanni sun nuna cewa tattaunawar ta hada da yiwuwar bai wa masu zuba jarin damar sayen hannun jari a matatun, wadanda suka dade ba su aiki yadda ya kamata ba duk da biliyoyin Daloli da aka kashe wajen gyaransu.

Matatar man Najeriya da ke Fatakwal
Jami'an NNPCL a matatar mai da ke Fatakwal. Hoto: NNPC Limited
Source: Twitter

Gwamnati ta ce bayan kusan shekaru uku na aiwatar da sauye-sauye, yanzu tana da niyyar kara karfafa zuba jari daga bangaren masu zaman kansu domin bunkasa tattalin arziki.

Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya kiyasta cewa tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa da kaso 4.4 cikin 100 a 2026, idan aka kwatanta da shekarar 2025.

Rahoton jaridar Tribune ya ce shekarar 2013, Najeriya ta sayar da kadarorin samar da wutar lantarki da rarraba wuta ga masu zaman kansu, a shekarar 2015 kuma an sayar da kamfanin sadarwa na gwamnati, Nitel.

Wani ya yi kundumbalar sayar da ofishin EFCC

A wani labarin, kun ji cewa wani matashi ya sanya Hedkwatar hukumar EFCC a kasuwa yana neman Naira miliyan 800.

Baya ga kudin da ya sanya na sayar da ofishin, matashin ya bukaci mai saye ya shirya ba shi la'adar Naira miliyan 120.

Hukumar EFFC da kanta ta yi wa matashin martani, lamarin da ya kara jan hankalin 'yan Najeriya a kafafen sada zumunta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng