Jerin kamfanoni 14 mallakin gwamnati da shugaba Buhari zai sayar saboda dalilai

Jerin kamfanoni 14 mallakin gwamnati da shugaba Buhari zai sayar saboda dalilai

A kokarin gwamnatin shugaba Buhari na farfado da kamfanoni mallakin gwamnati zuwa aiki tukur, gwamnati ta bayyana cewa, za ta sayar da wasu kamfanoni ko ba dasu ga masu zuba hannun jari a kasar. Legit.ng Hausa ta tattaro muku rahoto kan wadannan kamfanoni.

Abuja - Gwamnatin tarayya na shirin siyar da ko mika wasu kadarorin kasuwanci mallakin kasa ga masu saka hannun jari masu zaman kansu.

Wannan mataki, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, na daga cikin matakin da gwamnati ta dauka na farfado da kamfanonin a shekarar 2021 da kuma bayanta.

Ofishin Kamfanoni Mallakin Gwamnati (BPE) ya gayyaci masu son saka hannun jari don cin gajiyar tallafin da gwamnati ta gabatar da siyan cikin wadannan kamfanoni, haka jaridar Leadership ita ma ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Najeriya sun ragargaji yan ta'addan ISWAP a Borno, sun kashe 6

Jerin kamfanoni mallakin gwamnati da shugaba Buhari zai sayar a Najeriya
Gwamnati ta kudurta sayar da wasu kadarorinta ga masu zuba hannun jari | Hoto:The Bureau of Public Enterprises
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro muku jerin kamfanonin da gwamnati ta amince da yin wannan harkalla dasu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jerin Kamfanonin

 1. The Nigeria Integrated Power Projects (NIPPS) da ke a Calabar, Geregu, Omotosho da Benin (IHOVBOR)
 2. Transmission Company of Nigeria (TCN)
 3. Zungeru Hydro Plant
 4. Nigerian Postal Service (NIPOST)
 5. Abuja Environmental Protection Board (AEPB)
 6. The Nigeria Film Corporation (NFC)
 7. Federal Capital Territory Water Board
 8. Abuja International Conference Centre (AICC)
 9. Save Sugar Company
 10. Lagos International Trade Fair Complex (LTFC)
 11. Tafawa Balewa Square (TBS)
 12. River Basins Developments Authorities (RBDAS)
 13. Bank of Agriculture (BOA)
 14. The Nigeria Commodity Exchange (NCX)

Miyetti Allah za ta tura Fulani makiyaya Amurka domin a horar dasu kiwon zamani

A wani labarin daban, Amina Ajayi, Jakadiyar Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hure, kungiyar raya al'adu, ta gabatar da wani shiri mai karfi na horar da Fulani makiyaya akan kiwo na zamani, wanda aka misalta shi da kwatankwacin kiwo a Amurka.

Kara karanta wannan

Survival Fund: Gwamnati ta raba wa 'yan Najeriya sama da miliyan 1 kudade N56.8bn

Ajayi ta bayyana hakan ne a cikin jawabinta na karbar mukami biyo bayan nada ta a matsayin Jakadiyar Miyetti Allah a hedikwatar kungiyar ta kasa da ke Uke, Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.

Ta bayyana cewa rukunin farko na masu horaswa da malamai na makarantar Miyetti Allah Cattle Ranch Academy zai yi tafiya zuwa California a kasar Amurka, a farkon 2022, Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel