'Yan Majalisa Sun Kaure da Hayaniya, An Buga Muhawara a kan Aika Sakamakon Zabe

'Yan Majalisa Sun Kaure da Hayaniya, An Buga Muhawara a kan Aika Sakamakon Zabe

  • Bayan zazzafar muhawara da musayar yawu a kan dokar zaben Najeriya, Majalisar Dattawa ta kwantar da hankalin jama'a
  • Kafin zaman gaggawa da aka yi a ranar Talata, 10 ga watan Fabrairu, 2026, majalisar ba ta tilasta tura sakamakon kai tsaye ba
  • Sai dai bayan zanga-zangar jiga-jigan 'yan siyasa a Najeriya da suka hada da tsofaffin gwamnoni, majalisa ta sake matsaya a kan dokar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Takaddamar da ta dabaibaye amincewa da kudirin gyaran dokar zabe na 2026 a Majalisar Dattawa ta lafa bayan 'yan kwanaki.

An samu saukin lamarin ne a jiya, 11 ga watan Fabrairu, 2026 bayan Sanatoci sun sake duba sashe mai muhimmanci kan tura sakamakon zabe.

'Yan majalisa sun buga muhawara mai zafi a kan dokar zaben Najeriya
Wasu daga cikin 'yan majalisun Najeriya Hoto; House of Representatives
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa cewa Majalisar, wacce ta amince da tura sakamakon zabe ta hanyar lantarki zuwa manhajarta (IReV), ba ta tilasta a rika tura wa kai tsaye ba.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun riƙewa minista wuta a kan 'bacewar' kayan Gwamnatin Tarayya

Yadda Majalisa ta amince da dokar zabe

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa saboda Majalisar Dattawa ba ta amince da kalmar “tura sakamako kai tsaye” ba, kwamitin majalisun kasar sun sake zama domin a samu daidaito.

Gyaran Sashe na 60(3) da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta ya ce:

“Jami'in zaben zai tura sakamakon zabe kai tsaye daga kowace mazaba ta manhajar IRev, kuma za a aika sakamakon ne bayan an cika fam, an sa hannu tare da buga hatimi."

Sashen ya kara da cewa idan aka samu matsalar sadarwa har ba a iya tura sakamakon kai tsaye ba, fam din EC8A da aka sanya wa hannu da hatimi zai wadatar.

Hargitsi ya tashi a Majalisar Tarayya

Kafin fara zaman jiya, masu zanga-zanga sun sake taruwa a kofar Majalisar tarayya suna bukatar a saka sharadin tura sakamakon zaben kai tsaye a dokar.

An yi musayar zafafan ra'ayoyi a zaman majalisa game da dokar zabe
Wasu daga cikin Sanatocin Najeriya a zauren majalisa Hoto: The Nigerian Senate
Source: UGC

Tsohon gwamnan Ribas kuma tsohon Ministan Sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi, na daga cikin masu zanga-zangar, amma jami’an tsaro suka hana su shiga harabar majalisa.

Kara karanta wannan

'Dan majalisar Sokoto ya lale Naira miliyan 100, ya ba yara 2000 tallafin karatu

A cikin zauren majalisar kuwa, an buga muhawara mai zafi yayin da shugaban masu rinjaye, Mohammed Tahir Monguno, ya gabatar da kudirin sake duba Sashe na 60(3).

Ya nemi a soke matsayar farko tare da mayar da batun ga kwamitin majalisun dattawa da wakilai domin a sake dubawa.

Wannan ya haifar da rudani, inda wasu Sanatoci suka bukaci kada kuri’a kai tsaye bisa tanadin doka ta 72.

Daga bisani, bayan hayaniya da kiraye-kirayen oda, an amince da sabon gyaran da ya tanadi tura sakamako ta kai tsaye tare da tanadin fam din EC8A.

Majalisa ta sauya matsaya kan dokar zabe

A wani labarin, mun wallafa cewa Majalisar Dattawa ta sauya matsayarta kan kin amincewa da tanadin aika wa da sakamakon zabe kai tsaye ta hanyar yanar gizo.

Sanatoci sun janye matsayar da suka cimma a baya na kin amincewa da tura sakamakon zabe kai-tsaye daga rumfunan zabe zuwa shafin adana bayanan INEC.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Abba Moro, ne ya goyi bayan wannan kudiri, inda aka fito karara da neman a rika aika bayanan kai tsaye.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng