‘Da Sauran Rina Kaba’: DSS Ta ‘Gano’ Shirin Sake Kai Mummunan Hari a Kwara
- Hukumar DSS ta gargadi ‘yan sanda kan yiwuwar wani sabon hari a wasu yankunan kananan hukumomin jihar Kwara
- Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya kira taron gaggawa da shugabannin tsaro domin dakile sababbin barazana
- OPC ta bukaci ayyana dokar ta-baci kan tsaro a jihohin Yarabawa, tare da neman a bi sawun maharan a hukunta su
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara – Hukumar DSS reshen jihar Kwara ta fitar da gargadin tsaro ga rundunar ‘yan sandan jihar kan yiwuwar wani sabon hari a kauyen Gbabe da ke karamar hukumar Baruten.
Wannan gargadi ya zo ne kwanaki kadan bayan mummunan harin da aka kai a kauyen Woro da ke karamar hukumar Kaiama, inda aka kashe mutane da dama tare da tilasta wa wasu tserewa.

Source: Twitter
DSS ta yi gargadi ga 'yan sanda a Kwara

Kara karanta wannan
Karshen duniya: Ta kwabe wa yaro bayan zargin shi da hannu a garkuwa da mahaifinsa
Hakan na cikin wata wasika mai dauke da sa hannun Daraktan DSS na jihar, J.S. Adams, mai dauke da kwanan watan 5 ga Fabrairun 2026, cewar Punch.
Sanarwar ta yi nuni da taruwar wasu dauke da makamai da ake zargin ‘yan kungiyar Mamuda ne a kusa da Kiyoru, gundumar Gwanara.
Wasikar ta ce akwai yiwuwar kai hari kan al’ummar Gbabe, tare da jaddada bukatar kara tsaurara matakan tsaro domin kauce wa tabarbarewar doka da oda.
DSS ta kuma tunatar da tarihin ayyukan ta’addanci da kungiyoyin makamai ke yi a yankin Kainji, tare da bukatar jami’an tsaro su dauki matakan kariya cikin gaggawa.
Bayan wannan gargadi, mazauna yankin Baruten sun nuna damuwa, yayin da aka kara jibge jami’an tsaro a wasu sassan Kaiama bayan harin Woro.

Source: Twitter
Gwamna ya hada kan hukumomin tsaro a Kwara
Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya kira taron gaggawa na kwamitin tsaro a Ilorin domin duba halin tsaron jihar da kuma tsara hanyoyin dakile sababbin barazana.
Gwamnan ya ce taron na daga cikin matakan gaggawa da gwamnatin jihar ke dauka domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma kamar yadda shafinta ya wallafa a Facebook.
A bangaren kungiyar Oodua People’s Congress (OPC), ta bukaci gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma da sauran jihohin da ake magana da Yarbanci su ayyana dokar ta-baci kan tsaro.
Shugaban kwamitin rikon kwarya na OPC, Kazeem Lawal, ya ce dole ne a bi sawun wadanda suka aikata kisan gillar a Woro da Nuku domin cafke su tare da hukunta su.
OPC ta bayyana shirin kare yankin Yarbawa daga duk wani hari, tana mai cewa ba za ta zura ido ba yayin da ‘yan ta’adda ke addabar yankuna.
An 'hana' Shettima zuwa kauyen Woro
A wani labarin, Gwamnatin Jihar Kwara na fuskantar zargin hana Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ziyartar Woro, inda aka kashe sama da mutum 170.
Rahotanni sun nuna cewa an yaudari Shettima da cewa tafiya daga Ilorin zuwa Kaiama da nisa, alhali mummunan yanayin hanyar ne aka ɓoye masa.
Mazauna yankin sun zargi gwamnati da siyasantar da lamarin, suna cewa an ƙi bai wa iyalan waɗanda aka kashe damar ganawa da Kashim Shettima.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
