'Dan Majalisar Sokoto Ya Lale Naira Miliyan 100, Ya Ba Yara 2000 Tallafin Karatu
- Dan majalisar wakilai, Hon Bashir Usman Gorau ya kashe miliyoyin Naira domin tallafa wa dalibai akalla 2000 a jihar Sakkwato
- Daliban jihar da suka amfana sun fito daga jami’o’in tarayya, na jihohi da kuma makarantu masu zaman kansu a fadin kasar nan
- An gudanar da bikin rabon tallafin ne a jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, inda aka baje wani kaso daga cikin N100m da aka raba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto - 'Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gada-Goronyo ta tarayya a jihar Sakkwato, Hon. Bashir Usman Gorau, ya saukewa daliban mazabarsa kabakin arziki.
A ranar Litinin, 9 ga watan Fabrairu, 2026, ya raba jimillar Naira miliyan 101.4 a matsayin tallafin karatu ga dalibai sama da 2,000.

Source: Facebook
Bayanan fara raba tallafin na kunshe a cikin sakon da 'dan majalisar ya wallafa a shafin Facebook.
'Dan majalisar Sakkwato ya raba tallafin karatu
Daily Trust ta wallafa cewa wadanda suka samu tagomashin, dalibai ne daga mazabarsa Hon. Gorau da ke karatu a manyan makarantun gaba da sakandare a fadin Najeriya.
Daliban da suka ci gajiyar tallafin sun hada da masu karatu a jami’o’in tarayya, na jihohi da kuma na masu zaman kansu.
Dan majalisar ya bayyana cewa dalilin jinkirin da aka samu kafin rabon tallafin shi ne domin tabbatar da cewa an hada kowa da kowa ba tare da nuna bambanci ba.
An gudanar da bikin rabon tallafin ne a babban dakin taro na jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, inda daruruwan dalibai da iyayensu suka halarta domin karbar nasu tallafin.
'Zan bunkasa ilimi' - 'Dan majalisar Sakkwato
Gorau ya jaddada kudirinsa na ci gaba da tallafa wa harkar ilimi a mazabarsa, yana mai cewa ilimi shi ne ginshikin ci gaban tattalin arziki da al’umma baki daya.

Kara karanta wannan
Akwai kura: Dan majalisa ya tsallake rijiya da baya bayan fusatattun matasa sun farmake shi
Da yake jawabi a wajen bikin, Hon. Gorau ya bayyana ilimi a matsayin tubalin gina kowace kasa mai ci gaba.
Ya ce babu wata kasa da ta samu ci gaba a duniya face ta hanyar zuba jari da gaske wajen bunkasa rayuwar dan adam.
A cewarsa, tallafin da aka bayar ba kawai don saukaka wa dalibai wahala ba ne, amma wani bangare ne na shirin dogon zango domin bunkasa mazabar Gada-Goronyo.

Source: Facebook
Ya ce:
“Wannan (rabon tallafi) duk domin ci gaban mazabarmu ne. Duk wata kasa da ku ke gani ta ci gaba a duniya ta fara ne da gina dan Adam. Hanya daya tilo da za a bunkasa dan Adam ita ce ta ilimi, ingantacciyar kula da lafiya da kuma samar da hanyoyin dogaro da kai masu dorewa."
Ya kara da cewa bunkasa fannin ilimi zai taimaka wajen rage talauci, rashin aikin yi da kuma sauran matsalolin zamantakewa da ke addabar matasa
'Dan majalisa ya sha da kyar a Taraba
A wani labarin, mun wallafa cewa an shiga yanayin firgici a garin Gassol, jihar Taraba, bayan da wasu fusatattun matasa suka farmaki dan majalisar dokokin jihar, Hon. Abdullahi Muwalid.
Rahotanni sun nuna cewa matasan sun kai harin ne kan ayarin motocin dan majalisar, inda lamarin ya jefa al’umma cikin tashin hankali da fargabar tsoron halin da za a shiga.
An ce matasan sun dade suna nuna rashin jin dadinsu kan yadda dan majalisar ke tafiyar da wakilcinsa a majalisar dokokin jihar Taraba, amma ya tsallake rijiya da baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

