Ba Saban ba: Babbar Jam'iyyar Adawa Ta Yi wa Tinubu Tayin Dawowa Cikinta
- Mataimakin gwamnan Abia, Ikechukwu Emetu, ya ce jam'iyyarsu a shirye take ta karɓi Shugaba Bola Tinubu daga APC
- Emetu ya bayyana cewa LP jam’iyya ce mai buɗaɗɗen tsari, wadda ke karɓar kowa ba tare da la’akari da matsayinsa ko jam’iyyarsa ba
- Ya yi watsi da yunƙurin Julius Abure na ƙalubalantar hukuncin kotu, yana cewa LP ta riga ta wuce shi kuma ta koma karkashin sabon jagoranci
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Umuahia, Abia - Mataimakin Gwamnan Jihar Abia, Ikechukwu Emetu, ya tallata wa Bola Tinubu shiga jam'iyyar LP domin kawo ci gaba a Najeriya.
Emetu ya ce jam’iyyar LP za ta karɓi Shugaba Bola Ahmed Tinubu idan ya yanke shawarar barin APC.

Source: Twitter
An yi wa Tinubu tayin shiga LP
Ya bayyana hakan ne yayin gabatar da rahoton ci gaba da mika aiki ga kwamitin rikon kwarya na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Nenadi Usman, cewar Punch.
Emetu, wanda ke shugabantar kwamitin LP na rajista da sake tantance mambobi, ya ce jam’iyyar tana maraba da sababbin mambobi a kowane lokaci.
Ya mayar da martani ne kan tambaya ko Peter Obi zai iya komawa LP idan bai samu tikitin shugaban ƙasa a ADC ba.
A cewarsa, tsarin LP a bayyane yake kuma babu wanda aka haramta masa shiga jam’iyyar, komai matsayinsa a siyasa.
Emetu ya ce LP jam’iyya ce ta ƙasa baki ɗaya, ba wata ƙungiya ce ta sirri ba da ake hana mutane shiga.
Ya ƙara da cewa ko Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai iya shiga LP kafin zaɓen 2027, kuma za a karɓe shi hannu bibbiyu.
Da yake magana kan Julius Abure, Emetu ya ce ƙoƙarin ɗaukaka ƙara da yake yi ba shi da wani tasiri a yanzu.
Ya yi ba’a da cewa kotun da Abure zai iya kai ƙara ita ce filin wasan kwallon raga, yana mai cewa LP ta riga ta wuce shi.

Source: Facebook
Mataimakin gwamna ya tabo batun rigimar LP
Emetu ya tunatar da cewa kotun tarayya a Abuja ta yanke hukuncin cewa wa’adin Abure ya ƙare a matsayin shugaban LP na ƙasa.
Kotun ta umarci INEC da ta amince da kwamitin rikon kwarya ƙarƙashin Nenadi Usman har sai an gudanar da babban taron jam’iyyar.
Rikicin cikin gida ya tsananta ne bayan zaɓen 2023, inda aka samu shugabanci biyu da ƙorafe-ƙorafen kotuna masu yawa, cewar rahoton Tribune.
Bangaren da ke biyayya ga Gwamna Alex Otti ya yi maraba da hukuncin, yana kira da a yi sulhu domin ƙarfafa jam’iyyar adawa.
Gwamna Otti ya sha alwashi kan tazarce
Mun ba ku labarin cewa Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya halarci bikin ranar Aro ta shekarar 2025 da aka gudanar a karamar hukumar Arochukwu.
A jawabin da ya yi a wajen bikin, Gwamna Otti ya yi tsokaci kan batun sake tsayawa takara a zaben shekarar 2027.
Gwamna Otti ya nuna cewa bai da wata fargaba kan tazarce domin akwai abubuwan da za su sanya ya yi nasara cikin ruwan sanyi a zaben.
Asali: Legit.ng

