Gwamnati Ta Fadi Jihohin Arewa 2 da Za a Tura Dakarun Sojoji na Musamman
- Hafsan tsaron Najeriya Janar Olufemi Oluyede ya sanar da cewa za a tura dakaru na musamman zuwa Jihohin Kwara da Niger
- Ya bukaci a karfafa rundunar yan sanda da jami'an NSCDC domin su rika tsare yankunan da sojoji suka kwato daga yan ta'adda
- Janar din ya ce za a kaddamar da Operation Savannah Shield nan ba da jimawa ba domin karfafa tsaro a sassan Arewacin Najeriya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya sanar da cewa za a tura dakarun sojoji na musamman zuwa jihar Kwara da wasu sassa na jihar Niger.
Janar Oluyede ya bayyana hakan ne a yau Talata yayin zaman kare kasafin kuɗin shekarar 2026 a gaban kwamitin tsaro na majalisar wakilai.

Source: Facebook
Za a tura dakaru Neja da Kwara

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Bayan turo sojoji, an hango abin da Amurka za ta yi a zaben Najeriya na 2027
Hafsan tsaron ya bayyana cewa za a ƙaddamar da wani sabon rukunin dakarun haɗin gwiwa mai suna "Operation Savannah Shield" domin magance rashin tsaro a waɗannan yankuna, in ji rahoton Daily Trust.
A cewarsa, tuni aka tura dakaru na musamman zuwa jihohin Benue da Plateau, kuma za a dauko dakaru daga wadannan yankunan domin ƙarfafa wannan sabuwar rundunar.
"Za mu dauko dakaru da duk abubuwan da ake bukata daga sauran rundunoni don karfafa wannan rundunar da za a tura Neja da KWara, kuma za a tabbatar da tsaro a yankunan."
- Janar Olufemi Oluyede.
Ya yi nuni da cewa har yanzu ana fuskantar kalubalen tsaro mai yawa a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya duk da ana samun ci gaba a Arewa ta Gabas.
Karfafa 'yan sanda da NSCDC
Hafsan tsaron kasar ya jaddada cewa sojoji kaɗai ba za su iya magance matsalar tsaron Najeriya ba saboda ƙarancin dakaru.
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙarfafa rundunar ƴan sanda da kuma jami'an tsaro na farar hula, watau NSCDC cikin gaggawa.
Janar Oluyede ya bayyana cewa idan waɗannan hukumomin suna da ƙarfi, za su iya kare yankunan da sojoji suka kwato daga hannun ƴan ta'adda.

Kara karanta wannan
Maharan da suka kashe musulmai fiye da 100 a Kwara sun shiga uku, Sojoji sun fara cika umarni
Ya lura cewa sojoji ba sa samun hutu sakamakon yawan tura su daga wannan fage na yaƙi zuwa wani, wanda ka iya zama cikas gare su, in ji rahoton Vanguard.

Source: Twitter
Bukatar haɗin gwiwa da kasashen waje
Hafsan tsaron ya nuna cewa hedikwatar tsaron Najeriya tana kan haɗin gwiwa da ƙasashen da take ƙawance da su domin toshe giɓin da ake da shi a fannin samar da bayanan sirri.
Shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilai, Babajimi Benson, ya bayyana cewa ba za a iya magance matsalar tsaro ta hanyar amfani da ƙarfin makami kaɗai ba.
Ya buƙaci a samar da gyare-gyare a cikin hukumomin tsaro da kuma kyautata haɗin gwiwa tsakanin hukumomin daban-daban.
Benson ya yi gargaɗi cewa dole ne kasafin kuɗin da aka ware wa ɓangaren tsaro ya haifar da gagarumin sauyi da kowa zai gani a fadin ƙasar.
Amurka ta turo karin sojoji Najeriya
A wani labari, mun ruwaito cewa, Amurka ta aiko da wasu rukunin sojoji zuwa Najeriya, domin ƙara haɗin gwiwa wajen yaƙar ta’addanci a Yammacin Afirka.
Majiyoyi suka ce matakin ya biyo bayan yarjejeniya tsakanin kasashen biyu cewa ana buƙatar ƙarin matakai kan barazanar ’yan ta’adda.
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da zuwan sojojin, tana musanta zargin cin zarafin Kiristoci, tana cewa kowa na shan wahala daga matsalar tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng