Maharan da Suka Kashe Musulmai Fiye da 100 a Kwara Sun Shiga Uku, Sojoji Sun Fara Cika Umarni

Maharan da Suka Kashe Musulmai Fiye da 100 a Kwara Sun Shiga Uku, Sojoji Sun Fara Cika Umarni

  • Hedkwatar rundunar tsaron Najeriya ta sha alwashin kamo duk mai hannu a harin da aka kashe rayukan musulmi fiye da 100 a jihar Kwara
  • Bisa umarnin shugaban kasa, Bola Tinubu, hedkwatar tsaro ta kaddamar da sabuwar runduna da za ta kakkabe yan ta'adda a kwara da Neja
  • Daraktan sashen yada labaran ayyukan tsaro, Manjo Janar Michael Onoja ya ce sojoji ba za su runtsa ba sai an hukunta masu hannu a lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hedkwatar Tsaron Ƙasa (DHQ) ta lashi takobin kamo waɗanda suka iakata kisan kiyashi a garuruwa biyu a jihar Kwara don su girbi abin da suka shuka a gaban kotu.

Daraktan sashen yaɗa labaran ayyukan tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya isar da saƙon ta'aziyyar Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Olufemi Oluyede, zuwa ga iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma gwamnatin Kwara a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Sanata ya gama nazari, ya fito takarar gwamna a inuwar APC a zaben 2027

Dakarun soji.
Motocin yaki a hedkwatar tsaron Najeriya da ke Abuja Hoto: @DHQNigeria
Source: UGC

Harin Kwara ya tada Jami'an tsaro tsaye

Darektan ya bayyana cewa rundunar sojoji, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, suna iyakacin ƙoƙarinsu don tabbatar da tsaro ga kowane dan Najeriya, in ji rahoton Leadership.

Idan ba ku manta ba, wasu 'yan ta'adda sun kashe musulmai sama da 10 a wani hari da aka ce sun shafe sama da awanni 10 suna cin karensu babu babbaka a Woro da Nuku.

Onoja ya jaddada cewa jami'an tsaro ba za su yi kasa a guiwa ba wajen samar da yanayin da kowane ɗan Najeriya zai iya gudanar da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali ba tare da fargaba ba.

Babban Hafsan Tsaro ya yi ta'aziyya

"A kan wannan gaba, Babban Hafsan Tsaron Ƙasa yana isar da ta'aziyyarsa da juyayi ga Gwamnatin Jihar Kwara da iyalan waɗanda harin 'yan ta'adda ya shafa a ƙauyukan Woro da Nuku da ke ƙaramar hukumar Kaiama, wanda ya faru ranar 4 ga Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Ana batun dokar zabe, Ribadu ya aika da sakon gargadi ga 'yan siyasa

"Rundunar tsaron Najeriya za ta yi aiki kafada-da-kafada da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da an gurfanar da waɗanda suka aikata hakan a gaban shari'a."

- Manjo Janar Michael Onoja.

Sojoji sun fara cika umarnin Tinubu

Ya bayyana cewa, biyo bayan umarnin shugaban ƙasa, Hedkwatar Tsaro tare da haɗin gwiwar Hedkwatar Rundunar Sojin Ƙasa (AHQ) da sauran rassa, sun ƙaddamar da runduna ta musamman mai suna Operation Savanah Shield.

Wannan runduna za ta mayar da hankali ne wajen fatattakar maboyar 'yan ta'adda da ke addabar jihohin Kwara da Neja, kamar yadda The Nation ta kawo labarin.

A cewarsa, an kirkiro wannan sabuwar runduna ne daga cikin rundunar Operation Fansan Yamma, kuma an tsara ta ne don ƙarfafa tsaro a yankunnan.

Babban Hafsan Tsaro, Janar Oluyede.
Babban hafsan tsaron Najeriya, Olufemi Oluyede yana ganawa da yan jarida Hoto: @DHQNigeria
Source: Facebook

Tinubu ya tura bataliyar sojoji Kwara

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin tura bataliyar sojoji zuwa Woro a karamar hukumar Kaiama bayan harin yan ta'adda.

Bola Tinubu ya ce sabuwar rundunar sojojin da aka tura za ta jagoranci Operation Savannah Shield domin murkushe ‘yan ta’adda.

Shugaban kasar ya yi kakkausar suka kan harin, inda ya bayyana shi a matsayin abin kunya da rashin tausayi, yana mai kiran ‘yan ta’addan da marasa imani.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262