Kasuwar Singer: Peter Obi Ya Dura Kano, Ya Ambaci Kwankwaso da Abba
- Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya kai ziyarar jaje kasuwar Singer a Kano domin nuna alhini ga ’yan kasuwar da mummunar gobara ta shafa
- A cikin bayanin da ya yi, Peter Obi ya bayyana cewa gobarar ta jawo babbar asara ga ’yan kasuwar, jihar Kano da ma tattalin arzikin Nijeriya baki ɗaya
- Bayan ba da gudummuwa da ya yi, Obi ya yaba wa gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso bisa kokarin da suka yi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano – Jigo a jam’iyyar ADC, Peter Obi, ya bayyana alhininsa ga ’yan kasuwar Singer da ke Kano sakamakon gobarar da ta tashi kwanaki kaɗan da suka gabata.
An ce gobarar ta lalata kadarori da kayayyaki na miliyoyin Naira, lamarin da ya jefa ’yan kasuwar cikin damuwa da bukatar tallafi.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Peter Obi ya jinjinawa gwamnatin Kano da Abba Kabir ke jagoranta da kuma Sanata Rabiu Kwankwaso bisa tallafin da suka bayar.
Peter Obi ya je kasuwar Singer a Kano
A yayin ziyarar jaje da ya kai kasuwar, Peter Obi ya zagaya sassa daban-daban tare da abokan tafiyarsa, inda ya gana kai tsaye da ’yan kasuwar da abin ya shafa.
Obi ya tsaya yana kallon gine-ginen da suka kone da kuma wuraren da aka rasa kayayyaki, yana nuna alhini tare da jajanta wa waɗanda suka yi asarar dukiyoyinsu.
The Sun ta rahoto Obi ya ce zuwansa Kano da kansa ya nuna muhimmancin abin da ya faru da kuma yadda yake tausaya wa talakawa a fadin Najeriya.
Da yake jawabi ga ’yan kasuwar, Obi wanda ya nemi takarar shugaban kasa a 2023 ya ce:
“Ina so in fara da bayyana alhinina ga shugabannin wannan kasuwa da kuma ’yan kasuwar da suka yi asara. Mun zo nan domin mu ga abin da ya faru a kasuwar Singer.”

Kara karanta wannan
Alkawarin da Abba Kabir ya yi ga wadanda suka yi hatsari a Kano bayan jajanta musu
'An yi asara a kasuwar Singer' - Peter Obi
Peter Obi ya jaddada cewa gobarar ba ta tsaya ga lalata gine-gine da kayayyaki kaɗai ba, ya ce ta shafi tattalin arziki da rayuwar jama’a da dama.
A cewarsa:
“Wannan babbar asara ce. Idan ka kalli gine-ginen da kayayyaki da suka lalace, za ka fahimci girman abin da ya faru.”
Obi ya yabi Kwankwaso da Gwamna Abba
A cikin bayanin da ya yi, Peter Obi ya yaba wa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa tallafin da ya bayar, tare da cewa Rabiu Musa Kwankwaso ma ya tallafa.
Da yake magana a madadin ’yan kasuwar, shugaban kungiyar ’yan kasuwar Singer, Junaidu Mohammed, ya yi godiya ga Peter Obi da tawagarsa bisa ziyarar da suka kai.

Source: Facebook
An tarbi Kwankwaso a kasuwar Singer
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar jaje kasuwar Singer da ke Kano, inda dandazon jama'a suka tarbe shi.
Zuwan jagoran NNPP kasuwar da irin tarbar da aka masa ta jawo wasu magoya bayan Abba Kabir Yusuf fara kira a mayar da su wajen Kwankwaso.
Jim kadan bayan tafiyar Rabiu Kwankwaso daga kasuwar, gwamna Abba Kabir Yusuf ya je wajen da tawagarsa domin yi wa al'umma jaje.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

