Gwamnan Bauchi zai Hada Kai da Iran, Ya Fadi Harkokin da za Su Yi Tare
- Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana Iran a matsayin muhimmiyar ƙasa da za a iya haɗin gwiwa da ita a kasuwanci, noma da masana’antu
- Ya yi wannan jawabi ne a Abuja yayin bikin cikar Jamhuriyar Musulunci ta Iran shekara 47, inda ya nemi ƙarfafa hulɗar tattalin arziƙi da kasar Asiyar
- Rahoto ya nuna cewa jakadan Iran a Najeriya, Mahdavi Raja, ya jaddada aniyar ƙasarsa na faɗaɗa haɗin gwiwa da kasar nan a fannoni daban-daban
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yaba wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana bayyana ta a matsayin muhimmiyar kasa.
Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a Abuja, yayin bikin cikar Iran shekara 47 da kafa Jamhuriyar Musulunci, wanda ofishin jakadancin Iran a Nijeriya ya shirya.

Source: Facebook
Hadimin gwamna Bala Mohammed, Lawan Muazu Bauchi ya wallafa yadda taron ya gudana a wani sako da ya fitar a shafinsa na Facebook.
Gwamnan Bauchi ya yabi kasar Iran
Bala Mohammed ya ce, duk da “rade-radi da ra’ayoyi” da ake yadawa a duniya, Iran ta kasance kasa mai matukar muhimmanci.
Punch ta rahoto ya ce har zuwa yau, Iran na aika tallafi da shirye-shiryen ƙarfafa al’umma zuwa wurare da dama ba tare da neman yabo ba.
Gwamnan ya ƙara da cewa halartar sa bikin na nuna muhimmancin Iran a tsarin hulɗar duniya, musamman a dangantakarta da Afirka da sauran sassan duniya a fannin kasuwanci.
Ya ce ƙasashen biyu na da buƙatar koyi da juna ta hanyoyin da za su ƙarfafa dogaro da kai da tattalin arziƙi, yana mai tunatar da cewa Iran na da tsohuwar alaƙa da Najeriya.
Jihar Bauchi za ta hada kai da Iran
A bangaren kasuwanci da zuba jari, gwamnan ya bayyana cewa wani kamfanin Iran na shirin kafa babban aikin hako ma'adinai a jihar Bauchi.
Ya jaddada cewa kamfanin ba wai kawai zai ɗauki albarkatun ƙasa ya tafi da su ba ne, zai samar da cikakken tsari da zai daga darajar masana’antu a cikin jihar.
Gwamnan jihar ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa da masu zuba jari daga Iran a fannin noma da kiwon dabbobi.

Source: Facebook
Bala Mohammed ya ce Bauchi na da wadataccen ƙasar noma, yayin da Iran ke da fasahar da za ta iya ƙara yawan amfanin gona.
A nasa jawabin, Jakadan Iran a Nijeriya, Mahdavi Raja, ya tabbatar da ƙudirin ƙasarsa na faɗaɗa haɗin gwiwa da Najeriya, yana bayyana kasar nan a matsayin amintacciyar abokiya ga cigaba mai dorewa.
An kori kwamishina a gwamnatin Bauchi
A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya sanar da korar kwamishinan tsaro, Alhaji Ibrahim Gambo Galadima.
Alhaji Gambo Galadima ya rasa mukaminsa ne a wani garambawul ga gwamna Bala Mohammed ya gudanar a makon da muke ciki.
Gwamnatin Bala Mohammed ta bayyana cewa nan gaba kadan za ta sanar da wanda zai maye gurbin kwamishinan domin inganta tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

