Ana Wata sai ga Wata: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Coci, Sun Sace Masu Ibada
- Wasu yan bindiga sun sace masu ibada tara ciki har da mata da matasa yayin addu'o'in dare a wata majami'a dake Jihar Benue
- Shugaban karamar hukumar yankin ya bayyana cewa an tura jami'an tsaro domin bin sawun maharan tare da ceto masu ibadar
- Wannan harin na zuwa ne makonni biyu da sace wasu mutane biyu a yankin kuma aka biya Naira miliyan uku kafin aka sake su
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue - Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da masu ibada guda tara yayin da suke tsaka da gudanar da addu'o'in dare a cocin Katolikata ta St. John dake garin Ojije.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na daren ranar Asabar 7 ga watan Fubrairu a gundumar Utonkon dake ƙaramar hukumar Ado a jihar.

Source: Getty Images
'Yan bindiga sun sace masu ibada
Mazauna yankin sun bayyana cewa yawancin waɗanda aka sace ɗin mata ne da kuma matasa waɗanda ke cikin cocin lokacin da maharan suka afka musu, in ji rahoton Daily Trust.
Wannan hari ya jefa al'ummar Utonkon cikin fargaba da jimami, musamman ganin cewa an kai harin ne a cikin dakin bauta maimakon kan hanyoyi da maharan suka saba yi.
Sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar Ufia Development Association, Jude Onwe, ya nuna damuwa kan yadda hare-hare suka yawaita a yankin.
Ya tuna cewa makonni biyu da suka gabata, an sace wasu mutane biyu a wannan gari kuma an biya kuɗin fansa har Naira miliyan uku kafin aka sake su.
An zargi 'yan gari da kunnen kashi
Shugaban ƙaramar hukumar Ado, Sunday Oche, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa sun tura jami'an tsaro domin ceto waɗanda aka sace.
Oche ya soki mazauna yankin kan rashin bin shawarwarin da gwamnati ta bayar na daina gudanar da tarurrukan ibada na dare ba tare da sanar da jami'an tsaro ba.
Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Benue, DSP Udeme Edet, ya tabbatar da cewa an tura tawagar jami'ai na musamman yankin domin bin sawun maharan.

Source: Original
Jami'an tsaro sun bi sawun 'yan bindiga
A halin yanzu, jami'an tsaron suna aiki kan wasu hujjoji da suka samu, amma sun nuna cewa lokaci ya yi wuri da za a iya bayyana takamaiman waɗanda suka kai harin.
Duk da cewa mazauna yankin na cikin fargaba, shugaban ƙaramar hukumar ya ce ana nan ana ƙoƙarin tabbatar da cewa al'amura sun koma daidai, in ji rahoton Vanguard.
Rundunar ƴan sanda ta ba da tabbacin cewa za su yi duk mai yiwuwa domin ganin waɗanda aka sace sun dawo gidajensu cikin ƙoshin lafiya.
'Yan bindiga sun kashe mutane a Benue
A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu 'yan bindiga sun kashe mutane 13 tare da sace mata a harin da suka kai kasuwar Anwase dake jihar Benue.
Wannan hari yana zuwa ne kwanaki biyu bayan an kashe wasu mutane 16 a yankin Abande dake karamar hukumar Kwande, a jihar.
Jami’an tsaro sun isa yankin domin tabbatar da zaman lafiya yayin da daruruwan mutane ke tserewa daga gidajensu saboda tsoron hare haren.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


