Gwamnati Ta Gaza Cika Alkawari Watanni 11 da Kashe Hausawa a Uromi

Gwamnati Ta Gaza Cika Alkawari Watanni 11 da Kashe Hausawa a Uromi

  • Iyalan mafarautan Arewa 16 da aka kashe a Uromi a jihar Edo sun har yanzu ba su ji komai game da hakkin 'yan uwansu ba
  • Watanni 11 da suka gabata, mazauna Uromi tare da taimakon 'yan sa kai a jihar Edo sun tare mafaruta 16 daga Arewa, suka yi masu kisan gilla
  • Bayan mummunan kisan, Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya ziyarci Kano, inda ya yi alkawarin biyan diyya bayan faruwar lamarin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Iyalan mafarautan Arewa da aka kashe a wani mummunan hari a Uromi, tare da mutum daya da ya tsira, sun yi takaicin yadda gwamnati ta yi biris da su.

Sun bayyana cewa gwamnatin jihar Edo ba ta cika alkawarin biyan diyya ba, watanni 11 bayan faruwar lamarin da ya girgiza kasar nan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi kisa yayin da suka sace limami, ladan da wasu mutane

Yan uwan mafarautan da aka kashe a Uromi sun zargi gwamnati da watsi da su
Gwamnan Edo tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf a yayin ziyararsa zuwa Kano Hoto; Sanusi Bature D-Tofa
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa lamarin ya faru ne a ranar 28 ga Maris, 2025, lokacin da wasu ‘yan banga da matasan dauke da makamai suka kone mafarautan a hanyarsu ta zuwa Kano daga Ribas domin bikin Sallah.

Yadda aka kashe mafarautan Arewa a Uromi

Trust radio ta wallafa cewa an ce an tare motar mafarautan a hanyar Uromi/Obajana da ke karamar hukumar Esan North-East ta jihar Edo, inda aka zarge su da garkuwa da mutane.

Rahotanni sun ce maharan sun ja mafarautan daga cikin mota daya bayan daya, suka yi masu dukan kawo wuka, sannan suka banka musu wuta.

Dukkannin wadanda aka kashe ‘yan asalin kauyen Torankawa ne da ke karamar hukumar Bunkure a jihar Kano.

Iyalan mafarauta sun ce watanni 11 da kashe yan uwansu, babu wanda ya waiwaye su
Wasu daga cikin matasan da suka kashe mafarautan Kano, yadda aka yi jana'izar Hausawan da aka kashe a Uromi Hoto: Fahd Muhammad
Source: Facebook

Bayan faruwar lamarin, gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya kai ziyara ta ta’aziyya Torankawa tare da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An samu gawarwakin mawakan yabon addini 4 a wani irin yanayi

A wannan ziyara da ya kai, ya yi alkawarin biyan diyya da kuma tabbatar da an hukunta masu laifin.

A wancan lokaci, Okpebholo ya ce:

“Muna shirin biyan diyya ga duk wadanda abin ya shafa. Muna kuma tabbatar maku cewa za a gurfanar da masu laifin domin su fuskanci hukunci.”

Kisan Uromi: Gwamnati ta gaza biyan diyya

Sai dai kusan shekara guda bayan haka, iyalan sun ce babu wani abu da aka gani ko aka samu na daga cikin wannan alkawari.

Iyalan sun koka cewa duk da yawan alkawura da tabbaci daga bangaren gwamnati, babu wani abu da ya rage musu radadi ko ya saukaka halin da suke ciki.

Sun bukaci gwamnatocin Edo da Kano da su cika alkawuransu, suna mai cewa jinkirin da aka samu ya jefa masu shakkun za a yi masu adalci.

Kara karanta wannan

Ana zargin yaran Turji sun yi ajalin liman da basarake, jama'a sun tarwatse

Ibrahim Isa, mai shekaru 45, shi ne kadai wanda ya tsira daga harin. Mahaifin yara shida ne, kuma ya ce rayuwarsa ta shiga cikin kunci tun bayan dawowarsa gida.

Haka nan, Hauwa’u Isa, matar daya daga cikin wadanda aka kashe, ta roki gwamnatin Kano da ta taimaka mata da ‘ya’yanta uku.

Ta ce:

“Sun yi mana alkawarin diyya da adalci. Ina fata kada ya zama magana ta siyasa kawai.”

Malam Bala Dutse, mahaifin Amadu da aka kashe, ya gargadi gwamnati da kada ta bar lamarin ya mutu a shiru.

Abin da Gwamna ya ce bayan kisan Uromi

A baya, mun wallafa cewa Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya yi Allah wadai da kisan gilla da wasu matasa suka yi wa Hausawa ‘yan Arewa a garin Uromi.

Rahotanni sun bayyana cewa matasan sun kai hari kan ‘yan Arewan ne yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa gida domin shagalin Sallah, inda suka ƙona su da ransu.

A wata sanarwa da babban jami’in tsaro (CSO) na fadar gwamnatin Edo, SP Solomon Osaghale, ya fitar a ranar Juma’a, Gwamna Okpebholo ya bayyana kisan da rashin imani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng