'Abba bai Ci Amana ba,' An Tunawa Kwankwaso Abin da Ya Yi da Yana Mulkin Kano

'Abba bai Ci Amana ba,' An Tunawa Kwankwaso Abin da Ya Yi da Yana Mulkin Kano

  • Dr Yusuf Bello Danbatta ya bayyana cewa Gwamna Abba Yusuf bai ci amanar Sanata Rabiu Kwankwaso ba da ya koma jam'iyyar APC
  • Tsohon kwamishinan ya ce Kwankwaso ne ma ya kafa al'adar sauya sheka lokacin da ya bar PDP ya koma APC da ya na kan kujerar gwamna
  • Danbatta ya jaddada cewa Gwamna Abba kwararren mai gudanarwa ne wanda yake da ikon zabar jam'iyyar da yake so domin cigaban Kano

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Dr. Yusuf Bello Danbatta, daya daga cikin mambobin tafiyar Kwankwasiyya na farko, ya karyata ikirarin da wasu suke yi na cewar Gwamna Abba Yusuf ya yaudari Rabiu Musa Kwankwaso.

Tsohon kwamishinan tsare-tsaren tattalin arziki na jihar Kano a lokacin mulkin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ko kadan, Gwamna Abba bai yaudari jagoran Kwankwasiyya ba.

Kara karanta wannan

'Ba a sarki 2,' Tsohon kwamishina ya fadi dalilin batawar Abba da Kwankwaso a Kano

Dr. Danbatta ya yi magana game da alakar Abba da Kwankwaso bayan ya shiga APC.
Gwamna Abba Yusuf na mika wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kambun NEAPS da aka ba shi a ziyarar da ya kai gidansa a Abuja. Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Dr. Yusuf Danbatta, wanda tsohon dan takarar mataimakin gwamnan Kano karkashin PDP a 2023 ne, ya bayyana hakan a wata ta musamman da jaridar The Sun.

'Abba bai yaudari Kwankwaso ba' - Dr. Danbatta

Da aka tambaye shi ko Abba ya yaudari Kwankwaso da ya bar NNPP ya shiga jam'iyyar APC, Dr. Danbatta ya ce:

"Ba na tunanin haka. Wai don ya sauya sheka zuwa wata jam'iyya, Gwamna Abba bai yaudari Kwankwaso ba, saboda dole mu fahimci ma'anar yaudara.
"Shin Kwankwaso yana da iko kan Abba ne? A'a. Abba dan da Kwankwaso ya haifa ne? A'a. Daga abin da naji, Gwamna Abba tamkar abokin aikin Kwankwaso ne, amma irin wanda bai kai shi matsayi din na ba.
"Kwankwaso babban jami'i ne a lokacin da Abba yake aiki a WRECA. Sun kulla alaka ne saboda sun fahimci tasu ta zo daya.
"Sun zama abokan aiki, kuma Kwankwaso ya zama gwamnan Kano, ya cewa Abba ya zo ya taya shi gudanar da harkokinsa, kuma Abba ya yi hakan cikin kwarewa."

Kara karanta wannan

Ana batun tsige shi, Kwankwasiyya ta tura sako ga mataimakin gwamnan Kano

''Yan siyasa na da 'yancin sauya sheka'

Dr. Yusuf Danbatta ya ce zai iya bugun kirji ya fadawa duniya cewa Abba ya kware a harkar gudanarwa, saboda ya yi aiki tare da shi, ya san kwarewarsa a tafiyar da lamura.

Tsohon kwamishinan ya dage cewa, ko kusa Abba bai ci amanar Kwankwaso ba, domin ita siyasa rigar 'yanci ce, ba ta da masoyi ko abokin gaba na dindindin.

"Dan siyasa a Najeriya zai iya shiga kawance da kowace jam'iyya da ya ga ta dace da tsarinsa. Haka muke. yanzu na ba da labarin abin da ya fara tun daga 1979 har zuwa 2023. A duk kakar zabe a Kano, sai an sam wadanda suka sauya sheka. Wasu na nasara, wasu na faduwa.
"Me ya faru a lokacin da Ganduje ya so zama gwamnan Kano? Kwankwaso ne ya kirkiri R-APC a 2015, daga nan ya fara yaki da Ganduje."

- Dr. Yusuf Danbatta.

Dr. Yusuf Danbatta ya ce Kwankwaso ne ya fara shimfida akidar sauya sheka a Kano.
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana jawabi a wani taro. Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

'Shi ma Kwankwaso ya sauya sheka' - Danbatta

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP ta kara daukar zafi, ta nesanta kanta daga kalaman Kwankwaso

Dr. Danbatta ya kuma tuno lokacin da Kwankwaso yake gwamnan Kano a karkashin PDP, inda ya ce ya kirkiri rikici tsakanin Shugaba Jonathan da gwamnatin Kano, wanda ya sa aka hana 'yan asalin Kano mukamai a matakin tarayya.

Duk da wannan, ya ce:

"Amma a karshe me ya faru? Shi kwankwason dai shi ne ya zo ya sauya sheka, duk kwamishinoninsa da 'yan majalisar dokoki suka bi shi zuwa ina? APC!
"Don haka, wannan wata al'ada ce ta siyasa, ina da yakin shi kansa Kwankwaso, shi ne ya fara wannan sauya shekar. Abba yana kwamishina a lokacin, nima ina kwamishinan filaye. Dukkanmu muka sauya sheka zuwa APC kuma a karkashin PDP aka zabe mu.
"Haka a 2018, Kwankwaso yana kan kujerar sanata, da aka zaba karkashin APC, ya zo ya sauya sheka ya koma jam'iyyar PDP."

A karshe, ya jaddada cewa bai kamata a riƙa zargin Gwamna Abba da cin amana ba, domin abin da ya aikata abu ne da ya saba faruwa a fagen siyasar ƙasar nan baki ɗaya.

'Ba a yin gwamna 2 a gari 1' - Dr. Danbatta

A wani labari, mun ruwaito cewa, Dr. Yusuf Bello Danbatta ya bayyana cewa sauya shekarar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC tarihi ne ya maimaita kansa.

Kara karanta wannan

Kano ta kara daukar zafi, an kalubalanci Kwankwaso kan wasu kwangilolin gwamnatin Abba

Ya ce kowane gwamna yana so ya samu cikakken ikon gudanar da mulkinsa domin ba a taba sarki biyu a gari daya a dukkan fadin duniya.

Danbatta ya bayyana cewa, ba zai taba yiwuwa a samu gwamna biyu a jiha daya ba, idan kuwa aka ce za a yi hakan, to ba za a taba samu zaman lafiya ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com