Wata Sabuwa: Nnamdi Kanu Ya ba 'Yan Ta'addan IPOB Umarni daga Kurkuku

Wata Sabuwa: Nnamdi Kanu Ya ba 'Yan Ta'addan IPOB Umarni daga Kurkuku

  • Haramtacciyar kungiyar IPOB ta ce shugabanta da ke kurkuku, Nnamdi Kanu, ya bayar da umarnin soke zaman-gida baki ɗaya a jihohin Kudu-maso-Gabas
  • Sanarwar ta ce an soke umarnin ne har abada, kuma za ta fara aiki daga Litinin, 9, Fabrairu, 2026, domin bai wa jama’a damar komawa harkokinsu
  • IPOB ta gargadi duk wanda zai yi ƙoƙarin tilasta zaman-gida bayan wannan umarni, tana mai cewa irin waɗannan mutane suna aiki ne saɓanin umarnin Kanu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. Jihar

Jihar Enugu – Kungiyar IPOB da gwamnatin Najeriya ta haramta, ta sanar da kawo ƙarshen umarnin zaman-gida da ake yi a jihohin Kudu-maso-Gabas na ƙasar.

Kungiyar ta bayyana cewa shugabanta da ke kurkuku, Nnamdi Kanu, ne ya bayar da umarnin soke zaman-gidar gaba ɗaya, tare da jaddada cewa matakin zai fara aiki daga Litinin, 9, Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Kanin Ado Aliero ya kai hari Katsina, sojoji sun gwabza fada da 'yan bindiga

Shugaban 'yan ta'addan IPOB, Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu a cikin kotu a Abuja. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa sanarwa ta zo ne a daidai lokacin da jama’a da ‘yan kasuwa a yankin ke fuskantar asara mai yawa sakamakon zaman-gida da aka shafe shekaru ana aiwatarwa.

Umarnin Nnamdi Kanu ga kungiyar IPOB

A cikin wata sanarwa da kakakin IPOB, Emma Powerful, ya aikawa manema labarai a ranar Lahadi, ya ce Nnamdi Kanu ya bayyana soke zaman-gidar a matsayin mataki na dindindin.

A cewarsa, umarnin ya fito kai tsaye daga Nnamdi Kanu, wanda ya ce ya ɗauki wannan matsaya ne domin tabbatar da cewa yara suna zuwa makaranta a duk ranakun Litinin, tare da bai wa jama’a damar gudanar da kasuwanci da sauran harkoki.

Vanguard ta wallafa cewa Emma Powerful ya ƙara da cewa wannan umarni yana nufin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin, musamman ganin yadda zaman-gida ya janyo cikas ga ilimi da tattalin arziki.

Gargadin da Nnamdi Kanu ya yi

Kakakin IPOB ya jaddada cewa duk wanda ya yi ƙoƙarin tilasta zaman-gida bayan wannan sanarwa, yana aiki ne kai tsaye saɓanin umarnin Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

Yadda ƴan ta'adda suka rubuta wa Sarki wasiƙu kan shirin hari kafin hallaka Musulmai a Kwara

Ya ce irin waɗannan mutane ba sa wakiltar muradun al’ummar yankin, yana mai kiran su “abokan gaba ga al’umma da kuma manufar Biafra.”

A cewarsa, IPOB ba za ta lamunci duk wani mataki na tsoratarwa ko gallaza wa jama’a da sunan aiwatar da zaman-gida ba, yana mai cewa za a fuskanci duk wanda ya kauce wa wannan sabon umarni.

Za a koma harkoki kamar da

Emma Powerful ya yi kira ga mazauna jihohin Kudu-maso-Gabas da su fito su buɗe shaguna, su tafi wuraren aikinsu, tare da tura ‘ya’yansu makaranta ba tare da tsoro ba.

Ya bayyana cewa soke zaman-gidan na nufin dawo da walwala da kwanciyar hankali a yankin, tare da bai wa jama’a damar mayar da hankali kan ci gaba da rayuwa ta yau da kullum.

Yadda aka rufe kasuwar Onitsha a Anambra
Kasuwar Onitsha a rufe a 2023 saboda umarnin Kanu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Moore ya yi batun raba Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa dan majalisar Amurka, Riley Moore ya yi gargagi kan masu kira da a raba Najeriya, yana mai cewa matakin na da hadari.

Moore ya bayyana cewa ziyarar aiki da ya kawo Najeriya ba ta da alaka da neman raba kasar sai domin duba halin da Kiristoci ke ciki.

Ya kara da cewa raba Najeriya zai kara dagula matsalar tsaro a kasar da jefa Kiristoci cikin karin wahala musamman a Arewacin kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng