Sojojin Amurka Sun Dura Fadar Shugaban Kasa a Abuja, Sun Hadu da Tinubu
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi wata babbar tawagar sojojin Amurka a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, a wani zama da aka gudanar
- Taron ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka, musamman dangane da yaƙi da ta’addanci
- Ziyarar ta kuma biyo bayan rahotannin tura wasu sojojin Amurka Najeriya da kuma muhawara kan matsayar Amurka game da batun ‘yancin addini
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi wata tawagar sojojin Amurka a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock, inda aka gudanar da wata ganawa ta musamman.
Tawagar ta Amurka ta zo ƙarƙashin jagorancin Kwamandan Rundunar Sojojin Amurka a Afirka (USAFRICOM), Janar Dagvin R. Anderson, tare da wasu jami’ai.

Source: Facebook
Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ganawar ta samu halartar manyan jami’an tsaron Najeriya.
Sojojin Amurka sun hadu da Tinubu
Sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar ta ce Shugaba Tinubu ya tarbi Janar Dagvin Anderson tare da babban jami'i a ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, Keith Heffern, da sauran mambobin tawagar a Aso Rock Villa.
A cewar sanarwar, taron ya gudana ne tare da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, da shugabannin rundunonin tsaron ƙasa.
Sai dai Punch ta wallafa cewa ba a bayyana cikakkun bayanai kan abin da aka tattauna a ganawar ba, domin an gudanar da ita ne a sirrance.
Duk da haka, masu lura da al’amuran tsaro na ganin cewa ziyarar tana da alaƙa da ƙoƙarin ƙarfafa dangantakar tsaro tsakanin ƙasashen biyu, musamman a fannin yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci.

Kara karanta wannan
Yadda ƴan ta'adda suka rubuta wa Sarki wasiƙu kan shirin hari kafin hallaka Musulmai a Kwara
Alakar Najeriya da Amurka kan tsaro
Rahotanni sun nuna cewa ganawar ta biyo bayan labarin da ke cewa Amurka ta tura ƙaramar rundunar sojoji Najeriya a ranar 3, Fabrairu, 2026.
An bayyana zuwan sojojin a matsayin farkon kasancewar sojojin Amurka a Najeriya tun bayan hare-haren sama da aka kai a ranar Kirsimeti, 2025.
Hare-haren, a cewar bayanan da suka gabata, sun auna wuraren da ake zargin mayakan da ke da alaƙa da ƙungiyar ISIS suka kafa a dajin Bauni da ke Tangaza.
Manyan jami’an da suka halarta
A bangaren Najeriya, Shugaba Tinubu ya samu rakiyar NSA Nuhu Ribadu, Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya).
Babban Hafsan Tsaro Janar Olufemi Oluyede, Babban Hafsan Sojojin Ƙasa Laftanar Janar Waidi Shaibu, da Babban Hafsan Leken Asirin Tsaro Laftanar Janar Emmanuel Uandiandeye sun halarci zaman.

Source: Facebook
Haka kuma, Darakta-Janar na Hukumar Leken Asirin Ƙasa (NIA), Mohammed Mohammed, da Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Tosin Ajayi, duk sun halarci taron.
Amurka ta sa Najeriya a CPC
A wani labarin, mun kawo muku cewa a watan Oktoba, 2025, Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da tauye ‘yancin addini (CPC).
Gwamnatin Tarayya ta ƙi amincewa da wannan zargi, tana mai jaddada cewa ƙungiyoyin ta’addanci na kai hare-hare ne kan ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da addini ba.
Lamarin ya kai ga tura tawaga daga Najeriya zuwa Amurka, tare da kafa wani kwamiti na musamman tsakanin kasashen domin fahimtar juna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

