Ramadan: Kungiyar Masu Tumatir Sun Kwantar da Hankulan Ƴan Kasa kan Farashi
- Kungiyar manoman tumatir ta kasa, TGPMAN, ta ce ba a sa ran tashin farashin tumatir a watan Ramadan saboda yalwar amfanin gona bana
- Shugaban TGPMAN a Kaduna, Rabiu Zuntu, ya ce Ramadan na bana zai zo ne lokacin girbin tumatir, lamarin da zai kara yawansa a kasuwa
- Zuntu ya bayyana cewa karancin bukata yayin azumi da yalwar amfanin gona na iya haddasa faduwar farashin tumatir a jihohin Arewa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida..
Kaduna - Kungiyar Manoman Tumatir, Masu Sarrafawa da ’Yan Kasuwa ta Najeriya (TGPMAN) ta yi magana kan farashin tumatir a kasar
Kungiyar ta kwantar da hankalin jama’a kan yiwuwar tashin farashin tumatir da sauran kayan lambu a Ramadan mai zuwa.

Source: Twitter
Manoma tumatir sun magantu ana shirin Ramadan
Shugaban kungiyar a jihar Kaduna, Malam Rabiu Zuntu, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Lagos, cewar Vanguard.
Zuntu ya ce sabanin yadda farashin tumatir da barkono ke tashi a lokacin Ramadan a baya, bana al’amura za su bambanta saboda yalwar girbi da kuma lokacin da azumin ya zo.
Ya bayyana cewa a bara manoma sun sha wahala sakamakon faduwar farashin amfanin gona da kuma tsadar kayan noma, wanda ya rage musu riba sosai.
A cewarsa, farashin kayan lambu zai kara faduwa a wannan Ramadan, domin mutane na bukatar kayan lambu wajen buda baki, wanda ke karfafa noma.
Zuntu ya kara da cewa yawan samar da abinci gaba daya kan ragu yayin Ramadan, saboda Musulmai kan tsallake karin kumallo da rana lokacin azumi.
Ya ce idan samarwa ta yi yawa fiye da bukata, farashi kan ragu, yana mai jaddada cewa dokar kasuwa ta bukata da samarwa ce ke kayyade farashi.

Source: Facebook
Yadda manoman tumatir suka shiga wani hali
A cewarsa, a bara, faduwar farashin hatsi da sauran abinci ya sa manoma da dama a Arewa suka karkata zuwa noman kayan lambu.
Wannan ne ya haddasa yawan girbin tumatir, duk da kalubalen cutar Tuta Absoluta da ke lalata amfanin gona a wasu yankuna.
Ya ce yawanci, Ramadan kan fara ne a watan Afrilu, lokacin da amfanin gona ke karanci a kasuwa bayan karewar girbi, cewar rahoton Punch.
Sai dai ya ce a bana Ramadan zai fara ne a watan Fabrairu ya kare a Maris, wanda shi ne kololuwar lokacin girbin tumatir a Arewa.
Ya ce a jihohi kamar Kaduna, Kano da wasu yankuna da har yanzu ake girbi, farashin tumatir na iya kara faduwa sosai.
'Yan Najeriya sun yi martani kan hakan
Zuntu ya ce ’yan Najeriya kada su yi tsammanin tashin farashin tumatir a Ramadan, domin bukata za ta ragu yayin azumi.
Ya bayyana cewa a halin yanzu, kwandon tumatir mai nauyin kilo 50 na sayuwa tsakanin N7,000 zuwa N10,000 a Arewa.
A makonnin da suka gabata, an sayar da irin wannan kwando kan N5,000, sai dai a Kudanci farashin ya kai N18,000 zuwa N20,000 saboda sufuri.
A zantawar Legit Hausa da Malam Muntari Aliyu, wani mai wanki da guga a Unguwar Kagadama, jihar Bauchi, ya ce 'yan kasuwa sun saba kara kudin kaya idan azumi ya zo.
Malam Muntari ya ce:
"Mu dai ba mu san me sa ya suke yin haka ba, watakila ko don sun ga an fi bukatar kayan miya a lokacin ne shi yasa, ko da ya ke ba iya kayan miya ba, duk wani kayan masarufi suna kara masa kudi.
"A watan da ake so 'yan kasuwa, masu kudi da ma gwamnati su tausayawa talaka, su saukaka rayuwa don a yi azumi cikin sauki, amma a watan ne za ka ga wasu sun wasa kudinsu, suna dora riba mai yawa."
Malam Muntari ya yi kira ga 'yan kasuwa da su ji tsoron Allah su rika saukaka wa Musulmai a lokacin watan Ramadan ko Allah ya jikansu suma.
Rayuwar Farfesa mai sayar da tumatir
Kun ji cewa Farfesa Nasir Hassan-Wagini na jami'ar Katsina ya bayyana dalilin da ya sa aka ga yana sayar da kayan miya duk da matsayinsa.
Malamin jami'ar ya shaida cewa mahaifinsa manomi ne, kuma ya koyi noma tun yana yaro, don haka ne yake noman kayan lambu yanzu.
Maimakon jiran aikin gwamnati, Farfesa Hassan-Wagini ya bukaci matasa da dalibai su cire kunya su fara yin sana'o'in hannu.
Asali: Legit.ng


