Sauki Ya Kara Samuwa: Farashin Fetur Ya Karye a Wasu Gidajen Mai a Najeriya

Sauki Ya Kara Samuwa: Farashin Fetur Ya Karye a Wasu Gidajen Mai a Najeriya

  • An samu wasu gidajen mai a hanyar Legas zuwa Ibadan da suka rage farashin fetur zuwa kasa da 820 domin jan kwastomomi
  • Farashin fetur din da ake shigo da shi daga kasashen waje ya yi kasa da na matatar Dangote wanda hakan ya jawo gasa
  • Gidan mai na SGR ne ya fi kowa araha a halin yanzu inda yake sayar da lita daya akan 812 yayin da litar Dangote ta koma 799

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Gidajen mai dake kan babban hanyar Legas zuwa Ibadan sun shiga gasar rage farashin fetur domin riƙe masu sayen dake yankin.

Daga farashin ₦839 da aka sayar da lita a makon jiya, wasu gidajen mai a yankin Mowe zuwa Ibafo a Jihar Ogun sun rage farashin zuwa ₦815 yanzu.

'Yan kasuwa sun sauke farashin man fetur a wasu gidajen mai a Najeriya.
Mutane sun yi layi don sayen fetur a wani gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Wani bincike da jaridar The Punch ta gudanar ya nuna cewa gidajen mai da dama suna sayar da litar fetur ƙasa da farashin da matatar Dangote ta ba da shawara.

Wannan ragin ya biyo bayan ƙarin farashin da matatar Dangote ta yi daga ₦699 zuwa ₦799 a makonni biyu da suka gabata.

Sabon farashin fetur a gidajen mai

Binciken ya nuna yadda gidajen mai daban-daban suka rage farashin su domin doke abokan hamayyarsu kamar haka:

Gidan mai na SGR dake Mowe ya rage farashin sa zuwa ₦812 a kan kowace lita, wanda shine mafi araha a yankin a yau.

Gidan mai na Alade dake kusa da Ibafo yana sayar da litar fetur a kan ₦820, yayin da gidan mai na Habeeb ya sauko nashi farashin zuwa ₦819.

Gidajen mai na SAO dake Mowe da Lotto suna sayar da man a kan ₦825, farashi ɗaya da wanda gidan mai na Akiavic yake sayarwa.

Hukumar NIPCO tana sayar da fetur akan ₦828, yayin da gidajen mai na AP suke sayarwa tsakanin ₦830 zuwa ₦834 a kan kowace lita.

Farashin shigo da man fetur

A halin yanzu, farashin fetur ɗin da ake shigo da shi daga ƙasashen waje ya yi ƙasa da farashin da matatar Dangote take sayarwa.

Bayanan ƙungiyar MEMAN sun nuna cewa litar fetur ɗin da aka shigo da shi tana tsayawa akan ₦724 ne kacal a matsakaicin farashi, inji rahoton Ogun TV.

Wannan yana nufin farashin matatar Dangote ya fi na waje tsada da kusan ₦75, wanda hakan ya ba masu shigo da kaya damar yin gasa.

An samu gidajen man da ke sayar da fetur kasa da farashin da MRS take sayar da shi.
Gidan man kamfanin MRS, daya daga cikin manyan abokan huldar matatar Dangote. Hoto: @MRSOilNigeria
Source: Original

Farashin fetur a matatar Dangote

Duk da haka, wani jami'in matatar Dangote ya bayyana cewa yawancin gidajen man dake sayarwa da araha daga matatar suke dauko kayan.

A cewarsa, farashin ₦799 na Dangote ya haɗa da dukkan haraji, wanda hakan yake ba ƴan kasuwa damar rage farashi domin jan kwastomomi.

Wannan gasar ta tilasta wa gidajen mai na MRS dake ƙawance da Dangote rage farashin su daga ₦839 zuwa ₦825 domin su ci gaba da ciniki.

Litar fetur ta koma kasa da N800

A wani labarin kuma, mun rahoto cewa, an fara samawa ‘yan Najeriya sauki bayan wasu masu ma’ajiyar man fetur suka rage farashin fetur.

A Legas, wasu manyan ma’ajiyun mai sun sauke farashin fetur zuwa ƙasa da N800 kan kowace lita domin jawo kwastomomi.

A rumbun ajiyar man fetur na Aiteo, an sauke farashin litar man daga N797 zuwa N796. Ma'ajiyar mai ta Wosbab da Shellplux sun rage kudin daga N800 zuwa N798.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com