Ana Zargin Yaran Turji Sun Yi Ajalin Liman da Basarake, Jama’a Sun Tarwatse
- ’Yan bindiga sun kai hari kauyen Kiratawa da ke Sabon Birni a Sokoto, inda suka kashe limamin gari a harin da ya girgiza al’umma
- Maharan sun kuma tare hanyar Takatsaba a gadar Dangulbi, inda suka yi kwanton-bauna suka harbe mutum guda har lahira
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin da ya tilasta mazauna kauyen tserewa a yankin da dauki dogon lokaci ba tare da kai hari ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Da yammacin jiya Juma'a 6 ga watan Fabrairun 2026 wasu ’yan bindiga suka kai mummunan hari a kauyen Kiratawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.
Lamarin ya tayar da hankulan al'ummar yankin wanda aka ce harin ya yi sanadin rasa wani liman da kuma dagaci lamarin da ya tarwatsa jama'ar yankin baki daya.

Source: Original
Rahoton Bakatsine da ke kawo bayanai kan lamuran tsaro a Arewacin Najeriya shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X a yau Asabar 7 ga watan Fabrairun 2026.
Yadda yaran Turji ke tsula tsiya a Sokoto
Ana yawan samun hare-haren ta'addanci a yankunan Sokoto da ake alakantawa da yan bindiga masu biyayya ga Bello Turji da ya zama annoba a Arewacin Najeriya.
Bayan kisan limamin, maharan sun nufi hanyar Takatsaba inda suka yi kwanton-bauna a gadar Dangulbi, suka harbe wani mutum guda wanda ya rasa ransa nan take.
Rahotanni sun nuna cewa harin bai dauki lokaci mai tsawo ba kafin jami’an tsaro su isa yankin, lamarin da ya tilasta ’yan bindigar tserewa daga yankin domin tsira da rayukansu.

Source: Facebook
Tsawon lokaci da aka dauka babu hari
Majiyoyi sun bayyana cewa tun bayan kisan Kallamu, wani babban mataimaki ga shahararren dan bindiga Bello Turji, ba a sake samun wani hari a wannan hanya ba sai jiya.

Kara karanta wannan
Yadda ƴan ta'adda suka rubuta wa Sarki wasiƙu kan shirin hari kafin hallaka Musulmai a Kwara
Harin ya tayar da hankalin al’ummar yankin, inda ake kira ga hukumomi da su kara tsaurara matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a wadanda suke shan fama kan hare-haren.
Wasu majiyoyi suka ce ’yan bindiga da ake zargin suna biyayya ga shahararren jagoran ta’addanci Bello Turji sun kashe dagacin kauyen Magarau.
Haka nan, bayan hallaka babban limamin garin, an gano mazauna yankin na kauracewa kauyen baki ɗaya domin tsira da rayukansu.
Mazauna kauyen Magarau da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto sun tsere tare da barib gidajensu babu kowa bayan lalacewar kadarori da dama.
Sojoji sun fadi yadda Turji ke fama
Mun ba ku labari a baya cewa Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dan ta'adda, Bello Turji, wanda ake nema ruwa a jallo, na fuskantar matsin lamba mai tsanani daga dakarun.
Babban kwamandan rundunar hadin gwiwa ya ce bayanan sirri na nuna cewa Turji da mutanensa na ta kaura lokaci zuwa lokaci saboda firgita.
Sojoji sun kuma yi watsi da rade-radin cewa Turji na da iko da wasu kananan hukumomi, suna masu kiran hakan farfagandar ‘yan ta’adda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
