Abba Hikima: Jama'a Sun Ƙara Tara wa Haruna Kuɗi bayan Kashe Matarsa da Yara 6
- Bayan tallafin farko na Naira miliyan 25, jama’a sun ci gaba da turawa Mal Haruna Bashir kudi domin rage masa radadi
- Haruna Bashir na ya shiga tashin hankali bayan wani Umar da matasa biyu sun shiga gidansa, tare da kashe iyalinsa duka
- A tashin farko, jama'a sun bayar da gudunmawar N25m ta hannun fitaccen lauya Abba Hikima, yanzu kuma an samu kari
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Bayan tallafin farko da jama’a suka baiwa Malam Haruna Bashir Naira miliyan 25, mutane sun ci gaba da tura masa gudunmawa.
Fitaccen lauya, Barista Abba Hikima ne ya tabbatar da haka, inda ya bayyana cewa tuni aka hada wasu kudin bayan an ba shi taron farko

Source: Facebook
A sakon da Abba Hikima ya wallafa a shafinsa na Facebook, jama'a sun kara tura N453,000 domin a mika wa Haruna Bashir.
Jama'a sun kara taimaka wa Haruna Bashir
Daga cikin kudin da aka samu, Malam Haruna Bashir ya yi amfani da wani bangare wajen tallafawa dangin matarsa da sauran yan’uwansa.
Barista Abba Hikima ya bayyana cewa Haruna Bashir ya dauki matakin ne kamar yadda jamaa da dama suka bayar da shawara.

Source: Facebook
Magidancin dai ya gamu da iftila'i bayan wasu bata-garin matasa uku, wanda dangin matar ne sun shiga gidansa, tare da kashe Fatima Abubakar da yaransu shida.
Lamarin ya daga hankulan jama'a da shugabannin al'umma, kuma yanzu haka gwamnatin Kano ta fara shari'a da matasan da suka amsa kisa.
Jama'a sun yi wa Haruna Bashir addu'a
Mutanen da ke bin shafin Abba Hikima sun bayyana jin dadi a kan yadda jama'a ke ci gaba da taimakon Haruna Bashir da ya rasa iyalansa baki daya.

Kara karanta wannan
Rashin imani: Yadda 'yan ta'adda suka kira Sallah, suka kashe duk wanda ya zo Masallaci
Fatima Halilu Rabiu ta ce:
"Masha Allahu Allah ya jikan su da Rahma ya sakawa duk wadanda suka taimaka da alkairi."
Fadima Usman ta bayyana cewa:
"Ni a gani na da an hakura da wallafa maganan kudin nan haka, saboda kar abin yayi karfafa wa masu mugun tunani a maida abin hanyar neman arziki. Allah Ya kyauta, Allah jikan su Ya kara wa makusantan su hakuri."
Musbahu Adamu Aminu ya bayyana cewa:
"Allah ya biya ka da gidan aljanna, hakik da za mu samu irin ku a matsayin shugabanni da wallahi mun dace saboda irin yadda ka ke shiga da jibintar alamuran wanda yake cikin neman agaji. Muna addu'ar Allah ya kara maka sutura da karfin guiwa."
A zantawarta da Legit, Zainab Badamasi, ɗayabdaga cikin ƴan jaridan da suka ziyarci gidan Haruna a lokacin da aka yi kisan ta ce:
"Sai na ke ganin kawai kudin yana karba ne, amma fuskarsa ba annuri. Na tuna fuskokin matarsa da yaransa, har yanzu ina firgita ballantana shi. Allah Ya jikansu da rahama."
Daurawa ya ziyarci Haruna Bashir
A wani labarin, kun ji cewa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya kai ziyarar ta'aziyya ga Haruna Bashir da aka kashe matarsa da yaransu shida.
A yayin ziyarar, Sheikh Daurawa ya jajanta wa magidancin tare da addu'a da mamatan na samun rahamar Allah SWT, tare da kira da a hukunta mutanen da aka kama da laifi.
Ya bayyana cewa jami'an tsaro, kotu da gwamnati ne yanzu ke da alhakin tabbatar da cewa an bi hakkin Fatima Abubakar da yaranta, tare da kira ga jama'a da su taya jami'an tsaro da addu'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

