Tashin Hankali: An Gano Wani Bam da 'Yan Bindiga Suka Dasa Wa Mutane a Zamfara

Tashin Hankali: An Gano Wani Bam da 'Yan Bindiga Suka Dasa Wa Mutane a Zamfara

  • Ana zargin 'yan bindiga sun dasa bam a titin Danjibga zuwa Kuncin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara
  • Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa an gano bam din kuma jami'an tsaro sun yi nasarar kwance shi
  • Mai magana da yawun rundunar, Yazid Abubakar ya ce jami'an sashen kwance bam sun tsaftace hanyar, sun tabbatar babu wata barazana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Jami’an tsaro sun yi nasarar gano tare da lalata wani bam (IED) da ake zargin ’yan bindiga ne suka birne shi a kan hanyar Danjibga zuwa Kuncin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

Wannan aiki ya samu nasara ne sakamakon hadin gwiwar dakarun soji da jami’an ’yan sanda na sashen kwance bama-bamai (EOD–CBRN), da dakarun sashin yaki da garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Masu rufe hanya a sallar Juma'a sun jawo wa kansu, za a kai su kotu a Kano

Jihar Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Asabar, cewar rahoton Channels tv.

Jami'an tsaro sun kwance bam a Zamfara

A cikin wata sanarwar, kakakin rundunar ’yan sandan ya bayyana cewa aikin kwance bam din ya gudana ne ranar Juma’a karkashin jagorancin SP Abdulrazak Musa Hassan.

Ya kara da cewa jami’an sun yi amfani da dabarun kwarewa na zamani (RSP) wajen lalata bam din, wanda aka gano cewa na'u'in bama-baman da suke tashi ne idan aka taka su.

“An kwashe ragowar abubuwan da aka hada bam din da su domin gudanar da binciken kimiya na gano tushensu,” in ji Yazid Abubakar.

'Yan sanda sun kwantar da hankulan matafiya

Kakakin rundunar ya tabbatar da cewa bayan bincike na tsanaki da aka gudanar a yankin, an tabbatar da cewa hanyar yanzu ba ta da sauran wata barazana ta bam.

Kara karanta wannan

Ana fama da rashin tsaro, 'yan sanda sama da 5,000 za su ajiye aiki, an ji dalili

Bisa haka Yazid Abubakar ya ba da tabbacin cewa matafiya da mazauna yankin za su iya ci gaba da harkokinsu cikin natsuwa ba tare da wata fargaba ba.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da kasancewa masu sanya ido, sannan su taimaka wa jami’an tsaro da sahihan bayanai domin dakile ayyukan ta’addanci a fadin jihar.

Yan sanda.
Jami'an 'yan sanda a wurin da aka gano bam a Zamfara Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane, wadanda ke addabar yankunan karkara a Arewa maso Yamma da tsakiyar Najeriya.

Wadannan kungiyoyi suna da sansanoni a cikin manyan dazuzzuka da suka hada jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna, Sokoto, Kebbi, da Niger, inda suke fitowa domin kai hare-hare.

'Yan sanda sun kama bama-bamai a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Zamfara ta kama wani mutum mai shekaru 38 yana dauke da abubuwan fashewa har guda 954 a cikin motarsa.

Jami'an rundunar na musamman da ke yaƙi da hakar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba ne suka yi wannan kamen, biyo bayan samun sahihan bayanan sirri.

'yan sanda sun samu nasarar kama wanda ake zargin tare da kayayyakin yayin da yake tuka wata mota samfurin Toyota Corolla.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262