Masu Rufe Hanya a Sallar Juma’a Sun Jawo wa Kansu, Za a Kai Su Kotu a Kano

Masu Rufe Hanya a Sallar Juma’a Sun Jawo wa Kansu, Za a Kai Su Kotu a Kano

  • Hukumomin Kano sun nuna damuwa kan yawaitar rufe hanyoyi yayin sallar Juma’a, suna cewa lamarin na janyo cikas ga jama’a da sunan yin ibada
  • Shugaban Hukumar Shari’a ta Kano, Sheikh Abbas Daneji, ya ce an dauki matakin ne domin dakile dabi’ar tare hanyoyi da kuma inganta zaman lafiya
  • Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya goyi bayan matakin, yana cewa toshe hanyoyi yayin sallar Juma’a ya saba wa koyarwar Musulunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Hukumomi a jihar Kano sun fara nuna rashin jin dadi game da yawaitar tare hanoyoyi yayin salla da wasu masallatan Juma'a ke yi.

A garuruwa da dama musamman a Arewacin Najeriya, Musulmi da Kirista na rufe hanyoyi domin gudanar da ibadarsu a ranakun Juma'a da Asabar.

Gwmanatin Kan za ta dauki mataki kan masu rufe hanyoyi a sallar Juma'a
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Za a hukunta masu rufe hanya domin sallah

Kara karanta wannan

Yadda ƴan ta'adda suka rubuta wa Sarki wasiƙu kan shirin hari kafin hallaka Musulmai a Kwara

Shugaban hukumar shari'a ta Kano, Sheikh Abbas Abubakar Daneji ne ya bayyana hakan yayin taron majalisar zartarwar hukumar, cewar Premier Radio.

Daneji ya ce an dauki matakin ne domin nemo hanyoyin da za su ƙara ciyar da al'ummar jihar gaba da kuma dakile irin wadannan halaye.

Mutane da dama na yawan korafi game da yadda ake toshe hanyoyi tare da bata musu lokaci a duk lokacin da ake salla a masallacin Juma'a musamman a cikin birane.

‎Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da shugabannin hukumar ke cika shekara ɗaya da fara aiki a ofisoshinsu.

Gwamnatin Kano ta haramta toshe hanya yayin sallar Juma'a
Taswirar jihar Kano da ke yawan al'ummar Musulmi. Hoto: Legit.
Source: Original

Bashir Ahmad ya goyi bayan matakin

Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya bayyana goyon bayansa game da wannan mataki da cewa shi ne mafi alheri.

Bashir Ahmad ya bayyana haka ne a yau Asabar 7 ga watan Faburairun shekarar 2026 da muke ciki a shafinsa na X.

Ya ce hukumar ta gargadi al'umma da su guji rufe hanyoyi wanda hakan ke cutar da mutane tare da fuskantar hukunci idan suka saba umarnin.

Kara karanta wannan

Ana batun dokar zabe, Ribadu ya aika da sakon gargadi ga 'yan siyasa

Bashir ya yaba wa wannan mataki inda ya ce toshe hanyoyin al'umma yayin sallar Juma'a ya saba wa koyarwar Musulunci.

Ya ce:

"Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta umarci masallatan Juma’a da su daina rufe hanyoyin jama’a yayin gudanar da sallar Juma’a, tare da gargaɗin cewa duk masallacin da ya karya wannan umarni za a gurfanar da shi a gaban kotu.
"Wannan mataki abin yabawa ne matuƙa, domin toshe hanyoyin jama’a a lokacin sallah ya saɓa da koyarwar Musulunci, ya dace a yaɗa wannan saƙo sosai domin kowa ya sani."

Sallah a titi ya kusa tayar da fitina

Mun ba ku labarin cewa an samu fargaba a birnin Yenagoa da ke Bayelsa sadoda rufe babbar hanya domin za’ayi sallar Juma’a.

Hakan ya taso ne sakamakon hotuna da aka sanya a shafin labarai na yanar gizo, na wasu musulmai suna sallah a kan hanyar zuwa Asibitin Diete Koki.

Kiristocin Bayelsa sun kai korafi ga gwamnan jihar da ya gargadi musulman garin akan rufe hanya idan za su yi sallar Juma’a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.