Addinanci/Kabilanci: Sallah a kan titi ya kusa tayar da babbar fitina a jihar Bayelsa a makon jiya

Addinanci/Kabilanci: Sallah a kan titi ya kusa tayar da babbar fitina a jihar Bayelsa a makon jiya

- Fargaba a Yenogua sadoda an rufe babbar hanya dan za’ayi sallar Juma’a

- Hakan ya taso ne sakamakon hotuna da aka sanya a shafin labarai na yanar gizo, na wasu musulmai suna sallah akan hanyar zuwa Asibitin Diete Koki

- Kiristocin jihar sun kai korafi ga gwamnan jihar daya gargadi musulman garin akan rufe hanya idan zasuyi sallar Juma’a

Addinanci/Kabilanci: Sallah a kan titi ya kusa tayar da babbar fitina a jihar Bayelsa a makon jiya
Addinanci/Kabilanci: Sallah a kan titi ya kusa tayar da babbar fitina a jihar Bayelsa a makon jiya

Fargaba a jihar Bayelsa saboda an rufe babbar hanya dan za’ayi sallar juma’a, sakamakon wani hoto da aka sanya a shafin labarai na yanar gizo, na wasu musulmai suna sallah akan wani bangare na titin hanyar zuwa Asibitin Diete Koki.

Hoton ya janyo maganganun bacin rai daga mutanen jihar, na cewa an yadda musulmai su rufe hanya; 'Wannan ibada ta addini watau sallah akan hanya a hana wasu masu hakkin amfani da hanyar amfani da ita bazasu yadda ba kuma a daina.'

DUBA WANNAN: Wadanda zasu koma jam'iyyar SDP

A wata Pasta da aka sanya a gari anyi kira ne ga gwamnan Jihar ta Bayelsa, Mr Seriake Dickson, da kuma Chairman din karamar hukumar ta Yanaguwa, wanda ya fito daga Opolo, dasu gargadi musulmai dasu daina rufe hanya lokacin sallar Juma’a.

Duk da kace-nace din da akeyi amma ko mutum daya cikin jami’an gwamnati an rasa wanda keda niyyar yin wani jawabi akan al’amarin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng