Komai a Bayyane: Majalisar Shari'a Ta Tono Hadarin Shugaban INEC ga Musulmi

Komai a Bayyane: Majalisar Shari'a Ta Tono Hadarin Shugaban INEC ga Musulmi

  • Majalisar ƙoli kan harkokin shari’ar musulunci a Najeriya ta sake nanata kiranta na a tsige shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan, tana mai cewa ba zai iya yin adalci ba
  • Majalisar ta ce kiran ba shi da alaƙa da addini ko ƙabilanci, sai dai yana da nasaba da halayya, nagarta da wasu kalamai da ta ce shugaban INEC ya taɓa furtawa a baya
  • Ta jaddada cewa shugabancin hukumar zaɓe ta INEC na buƙatar mutumin da ba ya nuna wariya, bambanci ko kiyayya ga wani bangare na al’ummar da ke zaune a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Majalisar ƙoli kan harkokin shari’ar musulunci a Najeriya (SCSN) ta sake jaddada matsayarta na buƙatar a cire shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Joash Amupitan.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Dan majalisar Amurka ya yi magana kan batun raba Najeriya

Wannan matsaya ta fito ne a cikin wata sabuwar sanarwa da majalisar ta fitar, wanda sakatarenta, Nafi’u Baba Ahmad, ya sanya wa hannu, inda ta ce dole ne a fayyace cewa kiran ba shi da alaƙa da addini ko ƙabilanci.

Shugaban INEC da Sheikh Bashir Aliyu Umar
Shugaban INEC a hagu, Sheikh Bashir Aliyu Umar a dama. Hoto: INEC Nigeria| Dr Bashir Aliyu Umar
Source: Facebook

BBC Hausa ta wallafa cewa majalisar ta ce ta fitar da wannan sanarwa ne domin ƙarin bayani da fayyace matsayarta, biyo bayan wata sanarwa da ta fitar a ranar 28, Janairun 2026.

Dalilin neman cire shugaban INEC

A cewar majalisar, an sake fitar da takardar ne bayan da aka fahimci cewa wasu sun karkatar da abin da take nufi a baya.

Ta ce hakan ne ya sa aka zauna aka yanke shawarar sake fitar da wata sanarwa domin bayyana matsayarta ba tare da ruɗani ba.

Majalisar ta jaddada cewa batun da take magana a kai ba batun addini ba ne, sai dai batun nagarta, adalci da cancantar shugabanci.

Ta ce Najeriya ta gudanar da zaɓe tun daga samun ƴancin kai a 1960 zuwa yanzu, kuma ba a taɓa yin amfani da addini wajen amincewa ko ƙin amincewa da sakamakon zaɓe ba.

Tarihin shugabannin hukumar INEC

Sanarwar ta tunatar da cewa daga shugaban hukumar zaɓe na farko a 1960, Eyo Esua, zuwa yanzu, INEC ta samu shugabanni guda 13.

Kara karanta wannan

Yadda ƴan ta'adda suka rubuta wa Sarki wasiƙu kan shirin hari kafin hallaka Musulmai a Kwara

Rahotanni sun nuna cewa majalisar ta ce, Farfesa Attahiru Jega da Farfesa Mahmood Yakubu ne kaɗai musulmai daga cikinsu.

Ta ƙara da cewa duk da haka, ba a taɓa samun lokacin da Musulman Najeriya suka ƙi amincewa da zaɓe bisa bambancin addini ba, abin da ke nuna cewa kiran da ake yi a yanzu ba shi da alaka da addini.

Zargin da ake yi wa shugaban INEC

Majalisar ta ce dalilin neman cire Farfesa Amupitan yana da alaƙa da wasu abubuwa da ya aikata a baya, musamman wata takarda da ya jagoranci rubutawa a 2020.

A cewarta, a cikin takardar ya yi amfani da kalamai masu zafi da cin mutunci ga musulman Najeriya, yankin Arewa da Usman Ɗanfodio.

Ta ce a cikin takardar, shugaban INEC ya yi zargin ana yi wa Kiristocin Najeriya “kisan kiyashi”, sannan ya yi yunƙurin alaƙanta matsalar tsaro da jihadin Ɗanfodio na ƙarni na 19, abin da majalisar yunƙuri ne na tayar da zaune tsaye.

Majalisar ta ƙara da cewa abin takaici ne yadda aka kai irin wannan takarda ƙasashen waje, domin nuna Najeriya a matsayin ƙasa da ake tauye wa kiristoci 'yancin addini.

Kara karanta wannan

Bayan haduwar mutanen Abba da na Ganduje, an gwabza rikici a taron APC a Kano

Shugaban INEC da Bola Tinubu
Shugaban hukumar INEC na gaisawa da Bola Tinubu. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

A wani bidiyo da ya fitar a Facebook, Dr Bashir Aliyu Umar ya jaddada cewa buƙatar cire shugaban INEC ba ta da alaƙa da addini, yana mai cewa magana ce ta gaskiya, adalci da buƙatar kare sahihancin zaɓen Najeriya.

ADC ta ce za a yi magudi a zabe

A wani labarin, mun kawo muku cewa jam'iyyar adawa ta ADC ta yi zargin cewa APC mai mulki ta kamo hanyar magudin zabe a 2027.

Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi ne ya bayyana haka bayan majalisa ba ta amince da dokar tura sakamakon zabe ta yana gizo ba.

Bolaji Abdullahi ya ce jam'iyyar APC ta tsorata da halin da ta jefa 'yan Najeriya, kuma hakan ne ya sanya ta ke fargaba game da zabe mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng