Yaron Shekau da Ya Jagoranci Kashe Musulmai kusan 200 a Kwara
- An gano cewa kisan gillar da aka yi wa Musumai kusan 200 a Woro da ke karamar hukumar Kaiama ta jihar Kwara, ba lamari ne na bazata ba
- Rahotanni sun danganta harin da Abubakar Saidu, wanda aka fi sani da Sadiku, wani babban dan ta'adda da ke da alaka da Abubakar Shekau
- Masana tsaro sun ce kwararan shaidu na nuna yadda yankin Kainji ya zama sabuwar mafakar ‘yan ta’adda a Arewa ta Tsakiyan Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kwara – Harin da aka kai a kauyen Woro da ke karamar hukumar Kaiama ta jihar Kwara, wanda ya yi sanadin mutuwar Musulmai kusan 200, ya sake tayar da hankula game da yadda ta’addanci ke kara fadada.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa harin ba farmaki na bazata ba ne, wani bangare ne na tsari mai zurfi da ‘yan ta’adda suka shirya.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa masana tsaro sun ce jagoran harin, Abubakar Saidu, wanda aka fi sani da Sadiku, na da alaka da tsohon shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau.
Asalin Sadiku da alakarsa da Shekau
Rahotanni daga masana tsaro sun nuna cewa Sadiku ya fara fito wa fili tun kusan shekaru 12 da suka wuce, inda aka bayyana shi a matsayin amintaccen mataimaki ga marigayi shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, tun a shekarar 2014.
A wancan lokaci, an tura Sadiku zuwa jihar Neja domin fadada tasirin kungiyar Boko Haram daga Arewa maso Gabas zuwa wasu yankuna.

Source: Twitter
Wani mai sharhi kan yaki da ta’addanci a kafar X, MobilisingNigeria, ya bayyana cewa Shekau da kansa ne ya zabi Sadiku domin wakiltar muradun Boko Haram a yankin Neja.
Sadiku ya hada kai da 'yan bindiga
Bayan isa yankunan Arewa ta Tsakiya, Sadiku ya kulla alaka da wasu shahararrun shugabannin ‘yan bindiga, ciki har da Dogo Gide, inda suka hada kai wajen samun makamai da karfafa tasiri a karkara.
Sai dai daga bisani, sabani na akida ya balle tsakaninsu, lamarin da ya kai ga rikice-rikice da asarar rayuka a bangarorin biyu.
Bayan rabuwar kai da suka samu, Sadiku ya ja da baya zuwa cikin dazuzzukan yankin, inda ya kafa sansani a cikin dajin Kainji a watan Yuli, 2025.
Sabuwar Sambisa a Arewa ta Tsakiya
Masana tsaro sun bayyana dajin Kainji, wanda ya ratsa jihohin Neja da Kwara, a matsayin “sabuwar Sambisa” saboda yadda yake zama mafaka ga ‘yan ta’adda.
An ce dajin na bai wa ‘yan ta’adda damar daukar sababbin mambobi, boye makamai, da kai hare-hare kan al’ummomin karkara a jihohin Kwara, Neja, Kebbi da wasu sassan Kaduna.
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya wallafa a X cewa mutane 160 aka kashe, wasu rahotanni sun ce sun haura haka yayin da gwamnati ta tsaya a kan cewa rayuka 75 aka rasa.
Tinubu ya tura bataliyar sojoji Kwara
A wani rahoton, mun rahoto cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da kashe Musulmai kusan 200 a jihar Kwara.

Kara karanta wannan
Malami da fararen hula 4 da aka kama da zargin hannu a yunkurin juyin mulki a Najeriya
Bola Tinubu ya sanar da shirin aika bataliyar sojoji zuwa karamar hukumar da aka kashe mutanen domin kama wadanda suka aikata laifin.
Shugaban ya jaddada cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayuka, inda ya ce an kashe Musulman ne saboda sun ki yarda da bakuwar akida.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

