Atiku Abubakar Ya Fito Ya Yi Magana bayan Aisha Buhari Ta Kai Masa Ziyara a Saudiyya
- Tsohuwar uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari ta ziyarci tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a masaukinsa a kasar Saudiyya
- Aisha, wacce marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya rasu ya bari, da wasu daga cikin iyalanta ciki har da Hanan sun je Saudiyya ne domin yin Umrah
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana matukar farincinsa da wannan ziyara, ya tabbatar da ya hadu da Aisha ne da ya je ibada a Saudiyya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Saudi Arabia - Matar tsohon Shugaban Ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari, ta kai wa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ziyarar ban girma a ƙasar Saudiya.
Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya ta samu rakiyar wasu daga cikin iyalanta, ciki har da ɗiyarta, Hanan Muhammadu Buhari zuwa masaukin Atiku a kasa mai tsarki.

Source: Twitter
Atiku Abubakar ya karbi bakuncin Aisha Buhari
Atiku Abubakar, tsohon dan takarar shugaban kasa ya tabbatar da wannan ziyara a wani gajeren sako da ya wallafa a shafinsa na X da yammacin yau Juma'a, 6 ga watan Fabarairu, 2026.
Wazirin Adanawa ya wallafa hoton ziyarar a shafukansa na sada zumunta, inda ya bayyana cewa ya ji daɗin wannan karramawa da Aisha Buhari da iyalanta suka yi masa.
Bayanai sun nuna cewa Aisha Buhari da iyalanta sun je Saudiyya ne domin gudanar Umrah yayin da ake shirye-shiryen fara azumin watan Ramadan.
Abin da Atiku ya ce bayan ziyarar Aisha
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ya karbi bakuncin Aisha Buhari ne a lokacin da je Saudiyya ne domin yin aikin Umrah.
Atiku ya rubuta cewa:
“Na ji daɗin karɓar baƙuncin Hajiya Aisha Buhari, matar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, da ɗiyarta Hanan, da wasu daga cikin iyalanta yayin da suka ziyarce ni a Saudiyya.

Kara karanta wannan
Pantami ya sabunta rajistar zama dan APC, ya tuna shawarar da Buhari ya ba shi kan siyasar Gombe
"Kamar ni, tsohuwar Uwargidar Shugaban Ƙasar da iyalanta sun je Saudiyya ne domin gudanar da aikin Umrah."
Alakar Atiku da Muhammadu Buhari
Atiku da marigayi Buhari fitattun mutane ne a fagen siyasar Najeriya, waɗanda suka dauki tsawon shekaru ana damawa da su
Wazirin Adamawa da Marigayi Buhari sun fafata da juna a zaɓukan shugaban ƙasa daban-daban, amma wanda ya fi jan hankali shi ne lokacin da duka gwabza a zaben 2019.

Source: Twitter
Duk da saɓanin siyasarsu, duka mutanen biyu sukan fito fili su nuna girmamawa ga rawar da kowannensu ya taka a tafiyar dimuƙaraɗiyyar Najeriya.
Kamar dai Atiku, ita ma Aisha Buhari ƴar asalin Jihar Adamawa ce a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya.
Da gaske Pantami zai auri Aisha Buhari?
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya fito karara ya musanta rade-radin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa yana shirin auren Aisha Buhari.
Pantami, wanda ya yi aiki a gwamnatin marigayi Buhari, ya bayyana rade-radin a matsayin kirkirarren labari mara tushe, yana mai cewa abin ya ba shi mamaki.
A cewarsa, marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya kasance uba ne ga dukkan mutanen da suka yi aiki a gwamnatinsa, kuma wannan matsayi ne da ba zai taba canzawa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
