Bidiyo: Yadda Tinubu, Abba, Ganduje Suka Halarci Daurin Auren Ƴaƴan Matawalle 9
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya halarci daurin auren yayan karamin ministan tsaro Bello Matawalle a babban masallacin kasa dake Abuja
- Manyan jami’an gwamnati da gwamnonin jihohi kamar Abba Yusuf (Kano) sun halarci taron domin taya ministan murnar aurar da yayansa
- Sanata Barau Jibrin ya bayyanacewa Najeriya tana kan turbar cigaba karkashin jagorancin Tinubu yayin da ya roki 'yan kasar su dage da addu'a
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya halarci ɗaurin auren ƴaƴan karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, a babban masallacin kasa dake Abuja.
Daurin auren, wanda aka yi shi bayan sallar Jumu'ar yau, 6 ga Fabrairu, 2026, ya sami halartar manyan jami'an gwamnati da kuma jiga-jigan ƴan siyasar ƙasar nan.

Source: Twitter
Tinubu, Abba sun hadu a masallacin Abuja
Mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yaɗa labarai, Olusegun Dada, ne ya bayyana hakan ta hanyar wallafa faifan bidiyo a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Limami ya kalli Bola Tinubu, ya yi masa wasu addu'o'i a gaban manyan kasa a Abuja'
Dada Olusegun ya bayyana cewa:
“A yau Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya halarci ɗaurin auren ƴaƴan ministan tsaro wanda aka gudanar a babban masallacin kasa a Abuja.”
Bayan Shugaba Tinubu, sauran manyan baƙi da suka halarta sun haɗa da Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, Babban ministan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya) da tsohon Shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnonin jihohi da dama ma sun halarci daurin auren, ciki har da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano da Gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, Gwamna Uba Sani (Kaduna), Malam Umar Namadi (Jigawa) suna daga cikin jiga-jigan da suka taya ministan murnar aurar da ƴaƴansa a wannan gagarumin taron.
Bello Matawalle ya aurar da 'ya'ya 9
Jaridar Punch ta ruwaito cewa girman wannan taron ya janyo hankalin jama'a tun a watan Janairu, 2026 lokacin da katin gayyatar daurin auren ya bazu.
Ƴaƴan ministan tara da aka ɗaura wa aure a yau sun haɗa da Ibrahim, Suraj, Safiya, Maryam, Aisha, Fahad, Muhammad, Nana Firdausi, da Farida.
An gudanar da ɗaurin auren cikin tsauraran matakan tsaro sakamakon halartar shugaban kasa da sauran manyan madafun ikon ƙasar nan a masallacin.

Source: Twitter
Sanata Barau Jibrin ya yi maganar daurin auren
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya tabbatar da halartar taron a shafinsa na X, inda ya taya sababbin ma'auratan murna.
Sanata Barau ya bayyana cewa:
“Bayan sallar Juma'a, mun shaida ɗaurin auren ƴaƴan ministan tsaro, Bello Matawalle. Allah ya albarkaci wannan aure, ya ba su zaman lafiya.”
Ya ƙara da cewa Najeriya tana kan turbar ci gaba da wadata a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, sannan ya yi kira ga ƴan ƙasa.
Sanata Barau ya roƙi daukacin al'ummar ƙasar nan da su ci gaba da yi wa ƙasa addu'ar samun zaman lafiya da kuma ƙarin wadata.
Kalli bidiyon lokacin da Tinubu ya shiga masallacin a kasa:
An soki Akpabio da shiga masallaci da Tinubu
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan Najeriya sun yi ta korafi bayan ganin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio a cikin masallacin Juma'a tare da Shugaba Bola Tinubu.
'Yan kasar na korafi ne ganin cewa Akpabio kirista ne, don haka, a cewar wasu, babu dalilin da zai kai shi cikin masallaci a lokacin juma'a, in ba siyasa ba.
Baya ga Akpabio, Shugaba Bola Tinubu ya kuma hadu da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a masallacin, karon farko tun bayan karawarsu a zaben 2023.
Asali: Legit.ng

