Matasa Sun Taru Sun Kashe Tsohon Mai Gadin Fadar Mai Martaba Sarki, Sun Kona Gawarsa

Matasa Sun Taru Sun Kashe Tsohon Mai Gadin Fadar Mai Martaba Sarki, Sun Kona Gawarsa

  • Matasa sun taru sun kashe wani mutumi, Isma'il Zaria bisa zarginsa da hannu a kisan wani yaro a garin Keffi da ke jihar Nasarawa
  • Bayanai sun nuna cewa mutumin da aka kashe ya taba aiki a fadar Sarkin Keffi, kuma ya samu sabani da mahaifin yaron
  • Rundunar 'yan sandan Nasarawa ta ce jami'anta sun kai dauki wurin, amma sun tarar mutane sun kashe wanda ake zargi kuma sun kone gawarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nasarawa, Nigeria - Wasu fusatattun matasa a garin Keffi, Jihar Nasarawa, sun kashe wani mutum da ake zargi da hannu a kisan yaro, sannan suka cinnawa gawar wuta.

Mutumin da aka kashen, wanda aka gano sunansa Isma’ila Zaria, an bayyana cewa ya taba yin aikin gadi a fadar Mai Martaba Sarkin Keffi.

Kara karanta wannan

Mutanen da aka sace suna tsakiyar ibada a Kaduna sun bar hannun 'yan bindiga

Jihar Nasarawa.
Taswirar jihar Nasarawa da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta ce mazauna garin sun zargi Isma'il da hannu a kisan wani matashi mai suna Aliyu Muhammadu Lawal, wanda aka tsinci gawarsa a cikin wani rami.

Yadda matasa suka kashe Isma'il Zaria

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan banga ne suka fara kama Isma'il Zaria tare da tsare shi a ofishinsu.

Sai dai, dubban mutane sun mamaye ofishin, inda suka doke 'yan bangar, suka lalata ofishin, sannan suka lallasa wanda ake zargin har ya mutu kafin jami’an tsaro su iso.

Mahaifin yaron da aka kashe, Muhammadu Lawal, ya bayyana cewa ya taba samun sabani da wanda ake zargin (Isma'il Zaria) kan batun hayaniya da yake yi da daddare.

"Na tsinci gawar dana a cikin rami, an cire idanunsa, an yanka wuyansa, sannan akwai alamun an shake shi. Ba zan iya tabbatarwa ko rashin jituwar da muka yi a baya tana da alaka da kisan dana ba; na bar wa Allah komai," in ji shi.

Kara karanta wannan

Harin Kwara ya kara muni, adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya haura 80

Fadar Sarkin Keffi ta yi Allah-wadai

Wani mai rike da sarautar gargajiya a Keffi, Yahaya Ladan Shafale (Kakakin Sarkin Keffi), ya tabbatar da cewa fadar ta riga ta kori Isma'il Zaria daga aiki tun tuni.

Ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa yaron, yana mai cewa Keffi gari ne na tarihi kuma ba su taba ganin irin wannan zalunci ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa, SP Ramhan Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Wane mataki 'yan sanda suka dauka?

Ya ce sun samu kiran gaggawa ne da misalin karfe 12:30 na rana cewa an kama wani da ake zargi da kisan yaro.

Ya bayyana cewa:

"Kafin jami’ai su isa, gungun mutane sun riga sun kashe wanda ake zargin tare da kona shi. DPO na ya mani tare da jami'ansa sun samu nasarar kwantar da tarzoma tare da dauke gawar wanda aka konan zuwa babban asibitin Keffi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bankawa fadar mai martaba sarki wuta, sun kashe bayin Allah a Kwara

"A yanzu haka ana ci gaba da bincike domin gano gaskiyar lamarin game da kisan gillar da aka yi wa yaron da kuma daukar doka a hannu da mutane suka yi.
Jami'an yan sanda.
Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Getty Images

An kama mai tono gawa a makabarta

A wani labarin, kun ji cewa ‘yan sandan jihar Ogun sun cafke wani mutum mai suna Gafaru Rasaki bisa zargin tono gawa a makabarta da malakar kawunan mutane.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Babaseyi Oluseyi, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Oluseyi ya ce a lokacin da aka kama wanda ake zargin, an same shi da kawunan mutane hudu kuma bayan an yi masa tambayoyi ya amsa laifin da ake zarginsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262