Saudiyya Ta Kafe kan Bakarta, Musulmai Za Su Fuskanci Sharudda Masu Tsauri a Hajjin 2026

Saudiyya Ta Kafe kan Bakarta, Musulmai Za Su Fuskanci Sharudda Masu Tsauri a Hajjin 2026

  • Mahajjatan Najeriya da sauran kasashen duniya za su fuskanci tsauraran sharuddan da Saudiyya ta bullo da su a aikin Hajjin 2026
  • Hukumomin Saudiyya sun sake gargadin kasashe kan cika sharuddan biza a kan lokacin da aka gindaya domin gujewa matsala.
  • Ma'aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta nanata cewa ranar 8 ga watan Fabarairu, 2026, za ta rufe karbar bayanan mahajjata daga kowace kasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Saudi Arabia - Ma’aikatar Hajji da Umrah ta ƙasar Saudiya ta fitar da gargaɗi ga dukkan ƙasashen da ke shirin zuwa aikin Hajjin 2026 ciki har da Najeriya.

Ma'aikatar ta jaddada cewa 8 ga Fabrairu, 2026, ita ce rana ta ƙarshe ga kowace kasa ta kammala tura bayanan mahajjata da kuma shigar da su a shafin Nusuk Masar.

Alhazai.
Alhazan Najeriya da wasu kasashe a lokacin tsayiwar Arafa Hoto: Inside The Haramain
Source: Facebook

Leadership ta ce wannan mataki ne mai matukar muhimmanci ga fitar da biza, yayin da hukumomin Saudiyya suka sanya 20 ga Maris, 2025 a matsayin rana ta ƙarshe na kammala ayyukan biza baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Bayan kyautar N100m, gwamna Abba ya dauki matakai a kan gobara a kasuwar Kano

Sharuddan samun biza ta Hajjin 2026

A wani taro da ma'aikatar Hajji ta Saudiyya ta gudanar ranar 4 ga Fabrairu, Daraktan Hulda da Kasashe, Abdallah Awad Alshehri, ya lissafa wasu sharuɗɗan da dole kowace ƙasa ta cika kafin a ba mahajjatanta biza.

1. Biyan kudin hadaya

Hukumomin Saudiyya sun jaddada cewa dole ne a bayyana nau'in Hajjin da kowane mahajjaci zai yi (Tamattu’i, Qiran, ko Ifrad).

Mahajjatan da za su yi Tamattu’i da Qiran dole ne su biya kuɗin hadaya (dabbar layya) ta shafin yanzar gizo na Nusuk Masar, ban da waɗanda suka zaɓi yin azumi maimakon yanka dabba.

2. Yarjejeniyar kiwon lafiya

Dole ne kowace kasa ta kammala yarjejeniyar harkokin lafiya tare da kamfanonin lafiya masu lasisi da ke zaune a Saudiya ta hanyar shafin Nusuk Masar.

Ma'aikatar Hajji ta Saudiyya ta ce hakan zai ba da damar kowane mahajjaci ya samu ingantacciyar kulawar lafiya a lokacin Hajjin bana.

3. Masauki

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 76, kotu ta yi hukunci da gwamnatin Birtaniya ta kashe 'yan Najeriya 21

Sabuwar dokar Saudiya ta buƙaci kowace ƙasa ta tanadi ƙarin masauki a Makka na kashi 1% (1%) na adadin mahajjatanta.

Misali, ƙasar da take da mahajjata 40,000, dole ta kama ƙarin otal na mutum 400 wanda za a ajiye shi a matsayin tanadi don abubuwan da ba a zato.

4. Tantance fasfo

Duk mahajjaci ko jami’in da ba a tantance fasfonsa ba zuwa ranar 8 ga Fabrairu, akwai yiwuwar ba zai samu damar halartar Hajjin bana ba.

Saudiyya ta jaddada cewa dole ne kowace kasa ta bi tsari da ka'idojin da aka shimfida domin kaucewa rasa damar zuwa aikin Hajjin 2026, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Mahajjatan Najeriya.
Wasu daga cikin mahajjatan Najeriya a lokacin da za su shiga jirgin da zai kai su Saudiyya Hoto: @NAHCON
Source: Facebook

Kano ta tura tawaga Saudiyya

A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta fara wata ziyarar duba ayyuka a hukumance zuwa birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

Ziyarar na daga cikin matakan farko da hukumar ke ɗauka domin tabbatar da cewa an tanadi dukkan muhimman abubuwan da za su taimaka wajen gudanar da aikin Hajjin 2026 cikin tsari.

Babban manufar ziyarar ita ce duba wuraren masauki da kuma hanyoyin sufuri da za a yi amfani da su yayin aikin Hajji, domin tabbatar da cewa sun cika ka’idoji

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262