Abin Tausayi: Halin da Mutanen da Aka Sace Suna cikin Ibada Suka Shiga a Hannun Yan Bindiga

Abin Tausayi: Halin da Mutanen da Aka Sace Suna cikin Ibada Suka Shiga a Hannun Yan Bindiga

  • A jiya Alhamis G wamnatin Kaduna ta tabbatar da dawowar ragowar kiristocin da aka sace a coci uku a garin Kurmin Wali
  • 'Yan bindiga sun kai farmaki ne a lokacin da mutane ke tsakiyar ibada ranar Lahadi, inda suka tafi da masu ibada fiye da 177 zuwa daji
  • Bayan ceto mutanen, sun fara bayyana irin ukuba da azabar da suka sha hannun 'yan bindigar na tsawon makonni biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da cewa an ceto duka ragowar kiristocin da 'yan bindiga duka sace a Kurmin Wali da ke karamar hukumar Kajuru.

Wasu daga cikin mutanen da aka sace suna tsakiyar ibada sun yi bayanin mummunan halin da suka shiga da abubuwan da 'yan bindiga suka rika masu a cikin daji.

Kara karanta wannan

Masu ibada da aka sace a Kaduna, sun fadi yadda rayuwa ta kasance a hannun 'yan bindiga

Gwamnan Kaduna.
Wasu daga cikin kiristocin da aka ceto tare da Gwamna Uba Sani da mataimakiyarsa a gidan gwamnatin Kaduna Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Leadership ta tattaro cewa an sace mutanen ne tun ranar 18 ga watan Janairun 2026 yayin da suke tsaka da ibada, inda aka ceto su ranar Alhamis bayan kwashe mako biyu a tsare.

Halin da suka shiga a hannun 'yan bindiga

Daya daga cikin waɗanda suka dawo, Hosea Madami, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa sun fuskanci cin zarafi da azaba iri daban-dabanl'okacin da suke hannun masu garkuwa.

“Mun sha wahala sosai a daji. Sun doke ni a kaina da hannuwana, suna ciyar da mu kamar karnuka; abincin ma kaɗan suke zuba mana a hannu. Babu gishiri, don haka abincin ba shi da wani ɗanɗano,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa an tilasta musu yin tafiyar ƙasa na kwanaki shida a cikin daji ana dukan su da gora.

Yadda aka azabtar da mutanen da yunwa

Wata mata mai suna Rebecca Josiah, daga cikin wadanda aka ceto, ta bayyana cewa yunwa ita ce babban abin da ya fi addabar su.

Kara karanta wannan

Mutanen da aka sace suna tsakiyar ibada a Kaduna sun bar hannun 'yan bindiga

“Sau huɗu kawai na ci abinci a cikin mako biyu da muka yi a daji. Suna ba mu kunu ko tuwo a hannunmu. Idan abincin yana da zafi sosai, sai dai ka zuba shi a jikin tufafinka ka ci."

Ta ƙara da cewa sun yi tafiyar kwanaki ba takalmi, wanda hakan ya sa ƙafafunsu suka kumbura sakamakon taka ƙaya, yayin da ƙananan yara suka dinga kuka saboda tsananin yunwa.

Wata mata da ta buƙaci a sakaya sunanta ta ce ba a ba su damar yin wanka ba ko sau ɗaya, duk da cewa sun kwana kusa da kogi kuma idan mutum ya yi tari ko yara suka yi kuka, ‘yan bindigar suna dukan mutum, musamman maza.

Wata mai juna biyu, Theresa Irimiya, ta ce an sauƙaƙa mata saboda yanayinta, inda aka ƙyale ta ba a doke ta ba, sannan aka sallame ta da wuri tare da wasu yara.

Coci.
Cocin Ecwa da ke garin Kurmin Wali a jihar Kaduna Hoto: Ayuba John
Source: Facebook

An sako sauran mutanen Kaduna da aka sace

A wani rahoton, kun ji cewa yan bindiga sun sako ragowar kiristocin da suka yi garkuwa da su suna tsakiyar ibada a coci a garin Kurmin Wali, jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

'Mutane sun yi ta kansu,' Halin da ake ciki a garin da aka kashe sojan Najeriya

Wani jagoran al'umma wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida cewa an sako mutanen ne a daren jiya Laraba, kuma an wuce da su zuwa gudan gwamnatin Kaduna.

Har yanzu ba a tabbatar da ko an biya kuɗin fansa ba, ko kuma an ba wa masu garkuwar babura 17 da suka nema a baya kafin su sako mutanen ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262