An Yi Rashi: Tsohon Shugaban Babbar Jami'a a Arewacin Najeriya Ya Rasu

An Yi Rashi: Tsohon Shugaban Babbar Jami'a a Arewacin Najeriya Ya Rasu

  • An yi rashi na daya daga cikin manyan masana a fannin ilmi a Najeriya wanda ya bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen ci gaban kasa
  • Farfesa Buba Bajoga wanda ya taba shugabantar jami'ar ATBU ya yi bankwana da duniya yana da shekara 88
  • Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya mika sakon ta'aziyyarsa kan rasuwar marigayin, inda ya tuna da irin gudunmawar da ya bayar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Farfesa Buba Bajoga, fitaccen masani, gogaggen injiniya kuma dattijo a harkokin kasa, ya rasu.

Marigayi Farfesa Buba Bajoga ya rasu ne yana da shekaru 88 a kasar Birtaniya (United Kingdom).

Farfesa Buba Bajoga ya rasu
Marigayi Farfesa Buba Bajoga wanda ya taba shugabantar jami'ar ATBU Hoto: @Jameellamu
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa marigayin ya yi bankwana da duniya ne a ranar Alhamis, 5 ga watan Fabrairun 2026.

Wane ne Farfesa Buba Bajoga?

Marigayi Farfesa Bajoga ya kasance ƙwararren injiniya kuma malamin jami’a mai dogon tarihi na koyarwa da bincike da ya shafe shekaru da dama.

Kara karanta wannan

Bayan raba gari a siyasa, Abba da Kwankwaso sun gwada farin jininsu a Kano

Ya samu digirin farko (B.Sc.) a fannin injiniyancin lantarki daga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, a shekarar 1968, sannan ya samu digirin digirgir (PhD) daga Jami’ar jihar New York a 1972.

Marigayin ya rika samun karin girma a matsayinsa na malami a ABU har ya kai matsayin Farfesa na fannin Electrical Engineering a shekarar 1984.

Farfesa Bajoga ya taka rawa a jami'ar ATBU

Daga baya ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU), Bauchi, inda gudummawar da ya bayar ta taimaka matuƙa wajen samun cikakken ’yancin cin gashi kai ga jami’ar.

Haka kuma, ya yi wa ATBU hidima a matsayin shugaban jami'ar har na tsawon wa’adi biyu, daga 1984 zuwa 1994, sannan ya taɓa zama shugaban kungiyar shugabannin jami’o’i.

Marigayin ya rike manyan mukamai

Bayan fagen ilimi, Farfesa Bajoga ya bayar da gagarumar gudummawa a bangaren sadarwa da injiniyanci a Najeriya.

Ya riƙe manyan muƙamai na ƙasa, ciki har da darakta da shugaba a hukumar Nigerian Telecommunications Limited (NITEL).

Haka kuma ya yi aiki da hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) da majalisar kula da Injiniyoyi ta Najeriya (COREN), inda ya taimaka wajen tsara manufofi, dokoki da tsarin gudanarwa a fannin.

Kara karanta wannan

Yadda Sheikh Pantami ya ki amsa wa Tinubu da aka yi masa tayin mukaman gwamnati

Gwamna Inuwa ya yi ta'aziyya

A halin da ake ciki, gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi ta'aziyyar marigayin.

Gwamna Inuwa ya bayyana marigayi Farfesa Bajoga a matsayin fitaccen masani wanda ya yi suna a duniya, malami mai tsari da tarbiyya, kuma ɗa nagari na jihar Gombe wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga ilimi, hidimar jama’a da ci gaban kasa.

A cikin wata sanarwa da kakakinsa, Ismaila Uba Misilli, ya fitar a shafin Facebook, Gwamna Yahaya ya tuna da irin hidimar da marigayin ya yi wa jihar Gombe, musamman rawar da ya taka a matsayin shugaban kwamitin manyan makarantu a shekarar 2020.

Gwamna Inuwa ya yi ta'aziyyar Farfesa Buba Bajoga
Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook
"Farfesa Bajoga mutum ne mai hazaka ta musamman, gaskiya da tsananin kishin hidimtawa kasa. Shawarwarinsa, gogewarsa da kishin ƙasarsa sun ƙarfafa ƙoƙarinmu wajen sauya fasali da farfaɗo da ilimin gaba da sakandare a jihar Gombe.”

- Ismaila Uba Misilli

Ya ƙara da cewa za a ci gaba da tuna marigayi Farfesa Bajoga saboda tawali’unsa, ladabinsa da jajircewarsa ga ilimi da ci gaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Pantami ya sabunta rajistar zama dan APC, ya tuna shawarar da Buhari ya ba shi kan siyasar Gombe

Gwamna Yahaya ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, malamai da masana, da dukkan waɗanda rayuwarsa da ayyukansa suka shafa.

Surukin Bukola Saraki ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa mutuwa ta ratsa dangin tsohon shugaban majaliaae dattawa, Bukola Saraki.

Surukin Saraki kuma mai rike da sarautar Otunba na Legas kuma Lisa na Ife, Adekunle Ojora ya yi bankwana da duniya.

Otunba Ojora ya taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye martabar al’adun Yarbawa, tsarin masarauta da haɗin kan iyalan masu sarauta a Legas.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng