'Yan Sanda Sun Kama Wanda Ya Tono Kawunan Mutane a Makabarta
- ‘Yan sandan jihar Ogun sun cafke wani mutum mai suna Gafaru Rasaki bisa zargin tono gawa a makabarta da malakar kawunan mutane
- Rundunar ta ce an kama wanda ake zargin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka kai su ga gano shi a wani yanki na Sagamu
- ‘Yan sanda sun jaddada cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu tare da gargadin masu aikata irin wannan laifi a fadin jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ogun - Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wani mutum mai suna Gafaru Rasaki bisa zargin tono gawa a makabarta da kuma malakar kawunan mutane hudu.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Babaseyi Oluseyi, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Source: Original
Punch ta wallafa cewa ya ce jami’an ‘yan sanda sun samu nasarar cafke wanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri da suka tabbatar da aikata laifin.
An cafke matashi da kawunan mutane
A cewar rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, jami’an sashen Shagamu sun yi nasarar cafke Gafaru Rasaki ne a ranar 21, Janairu, 2026.
An bayyana cewa jami’an sun yi aiki ne bisa sahihan bayanan sirri da suka samu kan wani mutum da ake zargi da aikata laifin tono gawa.

Source: Facebook
Oluseyi ya ce a lokacin da aka kama wanda ake zargin, an same shi da kawunan mutane hudu. Bayan an yi masa tambayoyi da kuma gudanar da bincike mai zurfi, sai ya amsa cewa ya tono gawa ne daga wata makabarta.
Rundunar ta ce wannan aiki na nuna rashin girmama matattu kuma babban laifi ne a karkashin dokokin kasa. Oluseyi ya jaddada cewa duk wanda aka samu da aikata irin wannan laifi ba zai tsira daga hukunci ba.
Matakin da ya sanda suka dauka
Mai magana da yawun rundunar ya bayyana cewa an riga an kwace dukkan kayayyakin da aka samu a hannun wanda ake zargin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
Kakakin 'yan sanda ya ce da zarar an kammala binciken, za a gurfanar da Gafaru Rasaki a gaban kotu domin fuskantar hukunci daidai da laifinsa.
Ya yi gargadi ga duk masu hannu a laifuffukan tono gawa ko wulakanta matattu da cewa za a kama su, inda ya ce ba wannan ba ne karo na farko da rundunar ke cafke masu aikata irin wannan laifi ba a jihar.
A cewarsa, a watan da ya gabata, jami’an ‘yan sanda sun cafke wasu mutane uku a yankin Mowe bisa zargin hada baki da kuma mallakar sassan mutum ba bisa ka’ida ba.
An kama matashi da kwarangwal
A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta kama wani matashi da sassan jikin mutum a cikin motar da ya ke tafiya da ita.
Bayanai sun ce an gano kwarangwal din mutum a boye cikin motar Kazeem Ayegbo dake tafiya a kan hanyar Legas zuwa Ibadan.
Rundunar ta ce za ta gudanar da cikakken bincike domin kamo sauran masu alaka da Kazeem da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


