Bayan Kyautar N100m, Gwamna Abba Ya Dauki Matakai a kan Gobara a Kasuwar Kano

Bayan Kyautar N100m, Gwamna Abba Ya Dauki Matakai a kan Gobara a Kasuwar Kano

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyara kasuwar Singer domin jajanta wa ‘yan kasuwar da gobara ta shafa da ta jawo masu asarar miliyoyi
  • Bayan ziyarar da ya kai, Gwamna Abba ya bayyana cewa za a tallafa wa yan kasuwar tare dad daukan matakai don kare afkuwar haka a gaba
  • Gwamnati ta bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga waɗanda suka yi asara, sannan an sanar da aikin faɗaɗa da gyaran tituna a kasuwar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyara kasuwar Singer domin jajanta wa ‘yan kasuwar da gobarar da ta tashi kwanan nan ta shafa, inda ta lalata shaguna da kadarori masu yawa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kausasa harshe kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya dauki mataki

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi DawakinTofa, ya sanya wa hannu tare da fitarwa ga manema labarai a ranar Alhamis.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci kasuwar Singer
Gwamna Abba Kabir Yusuf a kasuwar Singer Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa gobarar da ta tashi da asubahin safiyar ranar Litinin 2 ga watan Fabrairu, 2026ta lalata manyan shaguna uku tare da jawo asarar miliyoyin Naira.

Gwamna ya ziyarci kasuwar Singer a Kano

21st Century Chronicle ta ruwaito cewa a yayin ziyarar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana matuƙar damuwa kan irin asarar da ‘yan kasuwar suka yi.

Sannan ya bayar da tabbatar masu da cewa gwamnatinsa za ta tsaya tsayin daka wajen tallafa masu da kula da su don rage radadin iftila'in da suka fada.

Gwamnan Kano ya bayar da gudunmawar kudi ga yan kasuwar Singer
Taswirar jihar Kano da aka samu gobara a kasuwar Singer Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sanarwar ta ce:

“Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da bayar da tallafin Naira miliyan 100 a matsayin agajin gaggawa ga waɗanda gobarar ta shafa."

An tarbi Gwamna Abba a kasuwar Kano

Daga cikin waɗanda suka tarbi gwamnan a yayin ziyarar akwai shugaban kasuwar Singer, Barista Junaidu Muhammad Zakari, dattijo a kasuwar, Alhaji Sabi’u Bako, da kuma mamallakin ginin da gobarar ta shafa, Alhaji Munzali Mazaf.

Kara karanta wannan

Bayan raba gari a siyasa, Abba da Kwankwaso sun gwada farin jininsu a Kano

Baya ga tallafin kuɗi, gwamnan ya ba da umarnin gaggauta faɗaɗa da gyaran tituna a cikin kasuwar Singer domin sauƙaƙa zirga-zirga da kuma inganta harkokin kasuwanci.

Sanarwar ta ce:

“An bayar da aikin faɗaɗa da gyaran tituna na N3bn a kan titunan Bello, Ado Bayero, Kandoki, Yolawa da Kwangiri, domin rage barazanar ambaliya da cunkoson ababen hawa a yankin kasuwannin Kano.”

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara da alƙawarin samar da hasken wutar lantarki mai amfani da hasken rana a kasuwar, tare da jaddada ƙudurin gwamnatinsa na zamanantar da kasuwannin Kano bisa tsarin sabunta birane da bunƙasar tattalin arziki.

Haka kuma, ya umarci kamfanonin da ke aikin titunan da su gaggauta tattara kayayyakinsu su fara aiki cikin kwanaki 10. domin a sama wa jama'a sauki a cikin gaggawa.

Shugabannin kasuwar da dattijai sun bayyana godiya ga gwamnan bisa wannan ziyara da kuma kyautatawarsa, inda suka bayyana tallafin a matsayin na kan lokaci kuma mai nuna tausayi.

Kano: Gobara ta tashi a kasuwar Singer

A baya, mun wallafa cewa kungiyar shugabannin kasuwanni Kano, KAMCHAFA, ta tabbatar da aukuwar wata mummunar gobara a kasuwar Singer da ke jihar.

Kara karanta wannan

Kalaman Kwankwaso na taimaka wa Abba Kabir a shari'ar 2019 sun jefa shi a matsala

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Ambasada Kabiru Musa Haruna, mai magana da yawun KAMCHAFA, ya fitar a ranar 2 ga watan Fabrairu, 2026.

A cikin sanarwar, KAMCHAFA ta bayyana alhini da baƙin ciki matuƙa kan lamarin, tare da jaddada cewa gobarar ta jefa ‘yan kasuwa da dama cikin mawuyacin hali.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng